Bayan watanni 3 da dakatad da shi, gwamnan jihar Bauchi ya mayar da Sarkin Misau kan kujerarsa

Bayan watanni 3 da dakatad da shi, gwamnan jihar Bauchi ya mayar da Sarkin Misau kan kujerarsa

- A faron shekarar nan, an yi rikice-rikice a karamar hukumar Misau ta jihar Bauchi

- A wannan rikicin, an yi asarar rayuka akalla guda tara kuma fiye da haka sun jigata

- An yi zargin Sarkin Misau na da hannu cikin rikici sai gwamnatin ta dakatad da shi

Gwamnan jihar Bauchi Bala Abdulkadir Mohammed, ya mayar da Sarkin Misau, Alhaji Ahmed Suleiman, kujerar mulkinsa bayan watanni uku da dakatad da shi.

Gwamnan ya mika takardar mayar da Sarkin Ahmed Suleiman ne a ranar Litinin, 12 ga watan Oktoba, 2020.

Sakataren gwamnati jihar Bauchi da wasu jami'an gwamnatin suka mika wa sarkin takardar kuma suka yi masa rakiya zuwa fadar sa, cewar BBC Hausa.

Shugaban ma'aikatar fadar gwamnatin Bauchi, Ladan Salihu, ya bayyana hakan a sakon da ya daura a shafinsa na Facebook.

A jawabin da hadiminsa, Sani Sabo yayi, yace: "Maigirma gwamnan jihar Bauchi Sen. Bala A. Muhammed CON. Yabada umurnin maida mai martaba sarkin misau Alh. Ahmed sulaiman MNI. Kujerarsa.

Allah yakarawa sarki lafiya da nisan kwana, Amin"

Bayan watanni 3 da dakatad da shi, gwamnan jihar Bauchi ya mayar da Sarkin Misau kan kujerarsa
Credit: Ladan Salihu
Asali: Facebook

DUBA NAN: SARS: IGP Adamu ya bayyana lokacin fara horar da sabon sashin 'yan sanda

A baya Legit ta kawo muku rahoton cewa Gwamman jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya sanar da dakatar da Sarkin Misau, Alhaji Ahmed Suleiman sakamakon rikicin da ya afku a gundumar Hardawa a karamar hukumar Misau da ya yi sanadin mutuwar mutum 9.

Wasu mutane da dama sun jikata sakamakon rikicin kamar yadda The punch ta ruwaito. Bayan sarkin, an kuma dakatar da Hakimin Chiromah da Dagajin Kauyen Zadawa ko wakilinsa.

Bayan watanni 3 da dakatad da shi, gwamnan jihar Bauchi ya mayar da Sarkin Misau kan kujerarsa
Credit: Ladan Salihu
Asali: Facebook

KU KARANTA: Hon. Onuoha ta kawo kudirin da zai bada damar amfani da wiwi wajen bincike

Sarkin Misau na daga cikin manyan sarakunan gargajiya a jihar Bauchi.

A 2015 ne dai aka naɗa Alhaji Ahmad Sulaiman Sarkin Misau, bayan rasuwar Sarki Muhammadu Manga.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel