Da duminsa: Kwamitin fadar shugaban kasa ya amince da bukatu 5 na masu zanga-zanga

Da duminsa: Kwamitin fadar shugaban kasa ya amince da bukatu 5 na masu zanga-zanga

- Shugaban 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya jagoranci taron masu ruwa da tsaki a kan kawo karshen SARS

- Kamar yadda takardar da aka fitar bayan taron ta bayyana, kwamitin fadar shugaban kasa ta amince da bukatu 5 na masu zanga-zangar

- Sun bukaci a daina amfani da hukumar wurin tsayar da zanga-zangar kuma a saki dukkan wadanda aka kama

Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya shugabanci taron masu ruwa da tsaki a kan tabbatar da bukatar kwamitin fadar shugaban kasa a kan gyara tsarin 'yan sanda.

Kamar yadda takardar wacce aka fitar bayan taron ta bayyana, masu ruwa da tsakin sun amince da bukatar masu zanga-zangar wanda ya hada da hana amfani da jami'an tsaro wurin dakatar da zanga-zanga tare da sakin wadanda aka kama.

Taron wanda ofishin sifeta janar na 'yan sandan Najeriya tare da hukumar kula da hakkin dan Adam suka shirya, ya samu halartar shugabanni da wakilan kungiyoyi masu zaman kansu, masu rajin kare hakkin dan Adam da sauransu.

Ma'aikatar kula da ayyukan 'yan sanda ta halarci taron inda ta tabbatar da cewa bukatu biyar na masu zanga-zangar sun dace a duba kuma gwamnati ta shawo kansu.

KU KARANTA: Sadio Mane: Hotuna da bidiyon motocin da ya mallaka da kuma darajarsu

Da duminsa: Kwamitin fadar shugaban kasa ya amince da bukatu 5 na masu zanga-zanga
Da duminsa: Kwamitin fadar shugaban kasa ya amince da bukatu 5 na masu zanga-zanga. Hoto daga @Dailynigerian
Asali: UGC

KU KARANTA: Bayan kwana 2 da 'yan bindiga suka kai hari Kaduna, shugabannin tsaro sun kai ziyara

A wani labari na daban, an tabbatar da mutuwar mutane 12 sannan mutane 7 sun samu munanan raunuka a wani kauye a jihar Kaduna ranar 11 ga watan Oktoban 2020.

Bayan harin da 'yan bindiga suka kaiwa kauyukan Kidandan da Kadai dake karamar hukumar Giwa dake jihar Kaduna ne aka tabbatar da mutuwar mutane 12 da mutane 7 da suka ji munanan raunuka.

Kamar yadda wadanda suka tsallake rijiya da baya suka tabbatar, wasu 'yan ta'adda da ke tafe da miyagun makamai, sun kaiwa kauyen Kidandan hari a ranar Juma'a.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel