SARS: IGP Adamu ya bayyana lokacin fara horar da sabon sashin 'yan sanda

SARS: IGP Adamu ya bayyana lokacin fara horar da sabon sashin 'yan sanda

- Shugaban 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya ce za a fara horar da sabon sashin da zai maye gurbin SARS

- Mohammed Adamu ya sanar da hakan yayin ziyarar da David Adeleke, fitaccen mawakin da aka fi sani da Davido ya kai masa

- Ya tabbatar da cewa sabon sashin za a gina shi ne da tubalin dabaru kuma ba za a maimaita kuskuren da tsohuwar rundunar ta yi ba

Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya bayyana cewa za a fara horar da wani sabon sashin da zai maye gurbin rundunar 'yan sanda ta musamman da aka rushe.

Adamu ya bayyana hakan a ranar Litinin bayan karbar David Adeleke, fitaccen mawaki, a ofishinsa.

Ya jaddada cewa rushe rundunar ya zama dole kuma sai an kara wani tsari domin maye gurbin wancan.

Sifeta Aminu ya ce sabon sashin za a gina shi ne ta hanyar tsari mai kyau, horarwar da ta dace kuma za su dinga aiki na musamman idan bukatar hakan ta taso.

Ya ce sabon sashin za a zuba masa jami'ai sabbi wadanda za a yi musu horarwa ta musamman ba wai tsoffin jami'ai ba.

Yayin sanar da cewa za a bai wa jama'a damar shiga sabon sashin, Adamu ya ce wannan ne karo na farko da aka yanke hukuncin rushe rundunar SARS.

Ya yi kira ga 'yan Najeriya da su kwantar da hankali yayin da ake cigaba da shawo kan matsalolin.

Ya ce ziyarar da Davido ya kai masa domin tattaunawa ita ce hanyar da ta dace wurin shawo kan matsalar da ake ciki. Ya tabbatar da cewa sabon sashin zai kiyaye duk wasu kuskure da jami'an SARS suka tafka.

"A jiya ne muka rushe SARS. Don haka masu zanga-zangar su kwantar da hankalinsu tare da bamu damar yin abinda ya dace.

"A yadda nake maka magana, zan cigaba da yi wa wasu kuma zan tattauna da kungiyoyi masu zaman kansu domin kafa sabon sashin," Adamu yace.

Ya yi alkawarin kaddamar da bincike a kan dukkan cin zarafin da jama'a ke kokawa a kai kuma za a dauka mataki.

KU KARANTA: Korarren kwamishinan Ganduje ya yi martani a kan dakatar da Dawisu Yakasai

SARS: IGP Adamu ya bayyana lokacin fara horar da sabon sashin 'yan sanda
SARS: IGP Adamu ya bayyana lokacin fara horar da sabon sashin 'yan sanda. Hoto daga @Dailynigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: 2023: Diyar Atiku Abubakar ta bayyana wanda za ta goyi baya ya shugabanci kasa

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar legas ta ce masu zanga-zanga sun harba jami'anta uku a ranar Litinin.

Jaridar The Cable ta wallafa yadda masu zanga-zanga suka rufe titunan Lekki, Surulere da Ikeja a jihar Legas inda suke bukatar a gyara tsarin ayyukan 'yan sanda.

Bayan zanga-zangar matasa a dukkan fadin kasar nan, Mohammed Adamu, Sifeta Janar na 'yan sandan Najeriya ya sanar da rushe rundunar 'yan sanda ta musamman ta yaki da fashi da makami.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel