Buhari ya assasa tubalin ginin Jami'ar Kungiyar JIBWIS a Jigawa

Buhari ya assasa tubalin ginin Jami'ar Kungiyar JIBWIS a Jigawa

- Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya assasa tubalin ginin Jami'ar Musulunci a jihar Jigawa

- Ministan Sadarwa Datka Isa Pantami ne ya wakilci Shugaba Muhammadu Buhari wurin taron

- Taron ya samu hallarcin gwamnoni, ƴan majalisa, masu sarautun gargajiya, manyan ma'aikatan gwamnati da sauransu

Buhari ya assasa tubalin ginin Jami'ar Kungiyar JIBWIS a Jigawa
Dakta Isa Pantami. Hoto daga @daily_nigerian
Asali: Twitter

Shugaba Muhammadu Buhari ya assasa tubalin ginin jami'ar musulunci ta As-Salam Global University, Hadejia, mallakar kungiyar Jama'atu Izalatul Bidi'ah Wa'iqamatis Sunnah, JIBWIS, jihar Jigawa.

DUBA WANNAN: Iyan Zazzau Bashir Aminu ya maka El-rufai a kotu saboda nada Bamalli sarki

Shugaban ƙasar da ministan sadarwa , Dakta Isa Pantami ya wakilta ya assasa tubalin ginin jami'ar a wurin taron.

Buhari shine baƙo na musamman wurin taron yayin da Sarkin Musulmi, Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar shine shugaban taron.

Kazalika, gwamnonin da suka hallarci taron sun hada da Muhammadu Badaru na jihar Jigawa da gwamnonin Sokoto, Kebbi, Katsina, Kano da tsaffin gwamnonin Zamfara.

Kazalika, ƴan majalisa, masu sarautun gargajiya, shugabannin addini, manyan ma'aikatan gwamnati da masu tallafawa al'umma sun hallarci taron.

KU KARANTA: Ganduje ya dakatar da hadiminsa Salihu Tanko Yakasai saboda sukar Buhari

Da ya ke jawabi wurin taron, shugaban JIBWIS na ƙasa, Sheikh Bala Lau ya sake jaddada cewa jami'ar ta al'ummar musulmi ce.

Ya ce: "Hakan yasa muke gayyatar musulmi a duk inda suke su zo su taimaka da duk abinda Allah ya sawwake musu."

"A yayin da muke fara wannan katafaren aikin, kowa ya sani cewa fatan mu shine kafa jami'ar ingantacciya da za ta amfani dukkan al'ummar musulmi. Da fatan Allah ya mana jagora. Amin."

A wani labarin daban, Alhaji Tanko Yakasai a ranar Litinin ya ce shugaban kasa, Muhammadu Buhari ba shi da ikon sauya fasalin tsarin mulkin Najeriya a karkashin kundin tsarin mulkin kasar.

Ya shawarci masu neman ganin an yi wa tsarin mulkin kasar garambawul su tabbatar wakilansu a majalisun jihohi da tarayya sun samar da dokokin da za su bada daman sauya mulkin kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel