Bidiyon yadda ma su zanga-zanga su ka kwaci dan sanda a hannun 'yan daba

Bidiyon yadda ma su zanga-zanga su ka kwaci dan sanda a hannun 'yan daba

- Har yanzu fusatattun matasa ba su daina gudanar da zanga-zangar neman soke rundunar SARS ba duk da an sanar da cewa an rushe rundunar

- Matasan sun cigaba da gudanar da zanga-zangar ne domin nuna rashin jin dadinsu a kan yadda ake tsare da wasu daga cikin abokansu da aka kama

- An samu barkewar rikici a tsakanin jami'an 'yan sanda da wasu daga cikin ma su zanga-zanga a wasu jihohi

A wani faifan bidiyo da jaridar The Cable ta wallafa an ga wasu ma su zanga-zanga sun hada kai tare da ceton wani dan sanda da wasu 'yan daba ke nufin cutarwa.

Duk da babban sifeton rundunar 'yan sanda (IGP) ya sanar da cewa an rushe rundunar SARS, har yanzu fusatattun matasa ba su daina fitowa domin gudanar da zanga-zanga ba.

Yayin zanga-zangar wasu batagarin matasa su ka biyo wani dan sanda da gudu, kamar yadda faifan bidiyon ya kunsa.

DUBA WANNAN: Kaduna: 'Yan bindiga sun kashe basarake Alhaji Musa Abubakar har gida

Dan sandan ya tsallake rijiya da baya bayan da ya ci karo da gungun matasa da ke gudanar da zanga-zanga wadanda su ka hana 'yan dabar da su ka biyoshi su cimmasa, bayan ya fada wani gida domin neman mafaka.

Bidiyon yadda ma su zanga-zanga su ka kwaci dan sanda a hannun 'yan daba
Wasu ma su zanga-zanga neman a rushe SARS
Asali: UGC

Legit.ng ta wallafa rahoton cewa, tsohon mataimakin shugaban, Atiku Abubakar, a ranar Lahadi, ya jinjinawa matasan Nigeria bisa jajurcewarsu na yakar zaluncin da rundunar 'yan sanda ke yi.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun harbe dan majalisa yayin da ya ziyarci mazabarsa domin halartar taron siyasa

Atiku, ya nuna gamsuwarsa, kan yadda matasan kasar suka hurawa rundunar 'yan sanda wuta har sai da ta rushe sashen rundunar na FSARS da ke yaki da fashi da makami.

A cikin wata sanarwa daga hadiminsa ta fuskar watsa alabarai Paul Ibe a Abuja a ranar Lahadi, Mr Abubakar ya ce rushe SARS alama ce ta bin tsarin wadatar da 'yan Nigeria ta fuskar tsaro.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel