Majalisar jihar Edo ta yi sabon kakaki, ta dakatar da tsohon kakakin

Majalisar jihar Edo ta yi sabon kakaki, ta dakatar da tsohon kakakin

- Wani kwarya-kwaryan rikici ya barke sakamakon tube kakakin majalisar jihar Edo, Hon Frank Okiye da 'yan majalisar 9 suka yi

- Sun tubeshi ne sakamakon zargin da ake yi masa na handama da wadaka da dukiyar al'umma

- Al'amarin ya faru kamar juyin mulki, inda ana tubesa, aka zabi wani sabon kakakin kuma aka rantsar dashi take-yanke

Anyi wani kwarya-kwaryan rikici a majalisar jihar Edo, inda cikin 'yan majalisu 10, 9 suka hada karfi da karfe wurin tube kakakin majalisar, Hon Frank Okiye, sakamakon zargin shi da ake yi da barnar dukiyar al'umma.

Bayan sun tube shi, take-yanke suka zabi wani sabon kakakin majalisar mai suna Hon. Marcus Onobun, wanda ke wakiltar mazabar Esan ta kudu.

Bayan an rantsar dashi take ya rushe duk wata kwamiti sannan ya soke duk wasu nade-nade da tsohon kakakin yayi, inda ya samar da wata kwamitin mutane 3 da zasu kula da shige da ficen kudi a majalisar.

An kuma dakatar da Okiye daga yin aikinsa, na tsawon makonni 3.

Al'amarin yayi kama da juyin mulki, inda duk wasu masu fadi a ji a jihar, kamar mataimakin gwamna, Philip shaibu, sakataren gwamnatin jihar, Osarodion Ogie da kuma mai bada shawara na musamman ga gwamna Godwin Obaseki, Hon Kabiru Adjoto suka hanzarta zuwa majalisar, amma sai suka tarar da majalisar a kulle saboda 'yan majalisar sun fara taron.

'Yan majalisar guda 9, sun hada da 'yan majalisa 3 na jam'iyyar APC da kuma sauran 7 da suka sanar da komawarsu PDP makon da ya gabata.

Al'amarin ya fara aukuwa ne tun bayan da duk 'yan majalisar suka zauna, Okiye ya umarci Magatakarda ya sanar da abinda za'a tattauna akai , take anan shugaban masu rinjaye, Hon Henry Okhuarobo mai wakiltar mazabar Ikpoba Okha ya tayar da maganar mai muhimmanci.

Inda yace mutane 9 a cikin 'yan majalisar sun sa hannu a korafin da aka yi akan Okiye.

An umarci Okiye da ya sauka daga kujerarsa ya bai wa mataimakin kakakin majalisar, Hon Roland Asoro damar cigaba da jagorantar zaman.

Prince Yekini Idaiye, dan majalisa mai wakiltar Akoko-Edo ya goyi bayan batun da Okhuarobo ya tayar.

KU KARANTA: COVID-19: An soke biyan kudin makaranta a dukkan makarantun Abuja

Majalisar jihar Edo ta yi sabon kakaki, ya dakatar da tsohon kakakin
Majalisar jihar Edo ta yi sabon kakaki, ya dakatar da tsohon kakakin. Hoto daga @Vanguard
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bayan kwasar gara, mutum daya ya mutu yayin da 6 ke kwance rai a hannun Allah

A wani labari na daban, Fadar shugaban kasa tace an sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari akan zanga-zangar da matasa ke yi saboda kashe-kashen da jami'an SARS ke yi.

Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa akan harkokin watsa labarai ya sanar da hakan a ranar Juma'a, 9 ga watan Oktoba, matasa na tsaka da zanga-zanga akan kisan wulakanci da 'yan sanda ke yi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel