Sunaye da ma'aikatu: Ganduje ya sauya wa manyan sakatarori 8 wurin aiki, ya nada 4 sabbi

Sunaye da ma'aikatu: Ganduje ya sauya wa manyan sakatarori 8 wurin aiki, ya nada 4 sabbi

- Gwamnan jihar kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya amince da canja wuraren ayyukan manyan sakatarorin gwamnatin jihar guda 8

- Sannan Ganduje ya kara daukar sababbin sakatarorin gwamnati 4 don tabbatar da cike kowanne gurbin aiki da kuma cigaban jihar

- Gwamnan ya shawarci musamman sababbin sakatarorin gwamnatin da su dage wurin yin aiki tukuru da amfani da fasahar zamani a ayyukansu

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya amince da canja wuraren ayyukan manyan sakatarorin gwamnati 8 da kuma daukan sababbin sakatarori 4.

Babban sakataren yada labaran jihar, Abba Anwar ne ya sanar da hakan a wata takarda ta ranar Lahadi a Kano.

Kamar yadda ya sanar, sakatarorin da aka canjawa wuraren aiki sun hada da Balarabe Karaye, wanda aka matsar daga ma'aikatar kasafi da tsari zuwa ta noma da albarkatu.

Sunaye da ma'aikatu: Ganduje ya sauya wa manyan sakatarori 8 wurin aiki, ya nada 4 sabbi
Sunaye da ma'aikatu: Ganduje ya sauya wa manyan sakatarori 8 wurin aiki, ya nada 4 sabbi. Hoto daga Dailynigerian
Asali: UGC

KU KARANTA: Matar aure ta haifa mace bayan watanni biyar da haihuwar tagwaye

Adamu Faragai, daga ma'aikatar noma da albarkatu zuwa ta Muhalli.

Binta Bala, wadda aka dauke daga ma'aikatar lafiya, zuwa ta kimiyya da fasaha.

Auwalu Sanda, daga ma'aikatar harkokin mata, zuwa ofishin mataimakin gwamnan jihar.

Amina Musa, daga ma'aikatar kimiyya da fasaha, zuwa ta lafiya.

Amina Aminu, daga ma'aikatar ruwa, zuwa ta harkokin mata

Hussaini Ganduje, daga ma'aikatar ayyuka na musamman zuwa ta ruwa.

An canja wa Abba Kailani wurin aiki, daga ofishin shugaban ma'aikata zuwa ma'aikatar habaka karkara.

Sabbabin sakatarorin gwamnatin da aka dauka,sun hada da Fatima Sarki, wadda aka dauka a ofishin shugaban ma'aikatan jihar.

Umar Albasu, sabon ma'aikaci ne, wanda aka dauka a matsayin sakataren gwamnati a ma'aikatar gidaje da sufuri.

Kabiru Magani da aka dauka a ma'aikatar ayyuka na musamman.

Abba Mustapha da aka dauka a ma'aikatar kasafi da tsari.

KU KARANTA: Bidiyon sallar Juma'a ta farko ta Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli

Gwamna Ganduje ya shawarci dukkan sakatarorin gwamnati da su dage wurin yin aiki tukuru da kuma rike kujerunsu kwarai don cigaban al'umma.

Gwamnan ya shawarcesu da su dage wurin amfani da fasahohin zamani wurin bunkasa ayyukan su.

A wani labari na daban, Daga watan Janairu zuwa yanzu, akalla mutane 36 sun mutu, 470 sun rasa gidajensu sakamakon ambaliyar ruwan sama a jihar Sokoto.

Mustapha Umar, shugaban hukumar wayar da kai da rage radadi ta jihar Sokoto (SEMA) ya bayyanar da hakan a wani taro na masu ruwa da tsaki a harkar ibtila'i a ranar Alhamis a jihar Sokoto.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel