'Yan bindiga sun kashe rayuka 12, mutum 9 sun jigata a Kaduna

'Yan bindiga sun kashe rayuka 12, mutum 9 sun jigata a Kaduna

- 'Yan bindiga sun kai wa Kauyukan Fatika da Kadai dake karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna hari a ranar Juma'a

- Sakamakon harin, sun kashe mutane 12, kuma sun ji wa mutane 7 munanan raunuka inda suka barsu a mummunan yanayi

- Hakimin Fatika, kuma Kaigaman Zazzau, Alhaji Nuhu Lawal Umar ya roki gwamnati da ta karo musu matakan tsaro a Fatika

An tabbatar da mutuwar mutane 12 sannan mutane 7 sun samu munanan raunuka a wani kauye a jihar Kaduna ranar 11 ga watan Oktoban 2020.

Bayan harin da 'yan bindiga suka kaiwa kauyukan Kidandan da Kadai dake karamar hukumar Giwa dake jihar Kaduna ne aka tabbatar da mutuwar mutane 12 da mutane 7 da suka ji munanan raunuka.

Kamar yadda wadanda suka tsallake rijiya da baya suka tabbatar, wasu 'yan ta'adda da ke tafe da miyagun makamai, sun kaiwa kauyen Kidandan hari a ranar Juma'a.

'Yan ta'addan sun kashe mutane 3 kuma sun ji wa mutane 4 munanan raunuka a kauyen Kadai ranar Asabar da daddare.

'Yan bindigan sun bar mutanen 4 a mawuyacin hali.

Dagacin Fatika, kuma Kaigaman Zazzau, Alhaji Nuhu Lawal Umar, ya roki gwamnati da ta taimaka ta karo jami'an tsaro don kula da rayukansu da dukiyoyin su.

Har yanzu dai ba'a ji komai ba daga wurin 'yan sandan.

KU KARANTA: EndSARS: Dawisu, hadimin Ganduje, ya yi wa Buhari wankin babban bargo

'Yan bindiga sun kashe rayuka 12, mutum 9 sun jigata a Kaduna
'Yan bindiga sun kashe rayuka 12, mutum 9 sun jigata a Kaduna. Hoto daga Vanguard
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ku yi rayuwa mai kyau, ko za ku samu makoma kyau - Obasanjo ya shawarci 'yan Najeriya

A wani labari na daban, Ministan matasa da wasanni, Sunday Dare, yace wasu 'yan ta'adda sun kaiwa fadar babban basarake dake Ogbomoso hari. Yace sun katse musu wani taro da suke yi tare da basaraken, Oba Oladunni Oyewumi a ranar Lahadi.

Jaridar The PUNCH ta tattaro bayanan yadda jami'an tsaro suka samu nasarar ceto ministan, basaraken da kuma sauran manyan mutane da suka halarci taron.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel