Ministan Buhari da babban basarake sun sha da kyar hannun 'yan daba

Ministan Buhari da babban basarake sun sha da kyar hannun 'yan daba

- Ministan matasa da wasanni, Sunday Dare, ya bayyana yadda wasu 'yan ta'adda suka kai hari fadar sarkin Ogbomoso suna tsaka da wani taro

- Yace 'yan ta'addan ba dalibai ko matasa bane, 'yan iskan gari ne da ke neman damar tadawa mutane hankula, saidai da taimakon 'yan sanda komai ya daidaita

- Duk da ministan, sarkin da sauran manyan mutane da suka halarci taron na cikin koshin lafiya, 'yan ta'addan sun farfasa kofofi, tagogi, kujeru, da sauran abubuwa a fadar

Ministan matasa da wasanni, Sunday Dare, yace wasu 'yan ta'adda sun kaiwa fadar babban basarake dake Ogbomoso hari.

Yace sun katse musu wani taro da suke yi tare da basaraken, Oba Oladunni Oyewumi a ranar Lahadi.

Jaridar The PUNCH ta tattaro bayanan yadda jami'an tsaro suka samu nasarar ceto ministan, basaraken da kuma sauran manyan mutane da suka halarci taron.

Amma kuma wakilinmu ya kasa tabbatar da ko 'yan ta'addan sun kaiwa ministan hari ne ko kuma wani daga cikin manyan mutanen.

Ministan ya sanar da yadda 'yan bindigan suka lalata abubuwa da dama a fadar.

Ya tabbatar da aukuwar lamarin ne a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, inda ya wallafa, "Wasu 'yan ta'addan Ogbomoso sun kai wa fadar Sarkin Ogbomoso hari, inda suka ritsa mu muna tsaka da taro.

"Sun fara rusa kofofi da tagogin kwalabe da duwatsu muna tsaka da taron. 'Yan sanda sun samu nasarar ceto na, sarkin da kuma manyan mutanen da suka halarci taron."

Ya kara da cewa, "Ba dalibai bane ko kuma matasa, 'yan iskan gari ne kawai da ke neman damar da za su tada hankulan jama'a. Sai dai saukin da aka samu shi ne, basu yi nasarar taba sarki, shugabannin Parapo, da kuma manyan mutanen da suka halarci taron ba."

Ministan yayi mamakin dalilin da zai sa su kai hari fadar sarkin, duk da Sarkin yana tabbatar da zaman lafiya a garin.

Dare ya kara da cewa, "Matasan Ogbomoso suna da bin doka. Amma wadannan 'yan ta'addan sun rinjaye su. Jami'an tsaro masu tarin yawa sun taho tun daga Ibadan, wasu kuma daga Ilorin, suna kula da fadar, kuma suna iyakar kokarinsu wurin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankalin jama'ar."

Jiya da yau, Sarkin Ogbomoso da kansa ya fito ya bada hakuri akan tada hankulan jama'a da 'yan ta'addan suka yi.

KU KARANTA: Da duminsa: Akeredelu ya lallasa Jegede, ya yi nasara da tazarar kuri'u masu yaw

Ministan Buhari da babban basarake sun sha da kyar hannun 'yan daba
Ministan Buhari da babban basarake sun sha da kyar hannun 'yan daba. Hoto daga @Mobilepunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: EndSARS: Abubuwa 5 da IGP ya sanar yayin soke rundunar SARS

A wani labari na daban, manema labarai, wakilan jam'iyyu da kuma masu lura da zabe sun tarwatse inda suka dinga neman maboya sakamakon ruwan wutar da ake musaya tsakanin 'yan sanda da 'yan daba.

Lamarin ya faru ne a makarantar firamare ta St Peter da ke Akure a ranar Asabar. Ana amfani da makarantar firamaren wurin tattara sakamakon zaben karamar hukumar Akure ta Kudu da ke jihar Ondo.

Jami'an hukumar zabe suna ta hada-hada domin fara tattara sakamakon zabe a lokacin da rikicin ya barke.

"Ku bar nan, ku tafi! Bai kamata ku tsaya ba," wasu 'yan sanda ke sanar da hakan ga manema labarai da masu lura da zabe yayin da suke mamaye kofar shiga wurin tattara sakamakon.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel