'Yan sanda sun damke mace mai ciki wata 9 da wasu matasa 2 a kan fashi da makami

'Yan sanda sun damke mace mai ciki wata 9 da wasu matasa 2 a kan fashi da makami

- Rundunar 'yan sandan jihar Edo ta cafke wasu 'yan fashi da makami uku a jihar

- A cikin 'yan fashin akwai mace mai tsohon ciki na watanni tara sai samari biyu

- Sun bayyana cewa da matar mai juna biyu suke amfani wurin cutar jama'a

Wasu mutum uku da suka hada da mata mai tsohon ciki sun shiga hannun rundunar 'yan sandan jihar Edo a kan zarginsu da ake yi da fashi da makami.

A yayin tabbatar da kamen ga manema labarai, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Chidi Nwabuzor, ya bada sunan wadanda aka damken da Jumoke Akanbieme, Osagiede Izevbokun da Godfrey Okonide.

A yayin bayyana yadda suke aikin, Nwabuzor ya ce mazan biyu su kan ajiye matar a gefen titi inda za ta nuna tamkar tana nakuda har jama'a su tsaya sannan sun kai musu hari.

A kan yadda aka kama su, kakakin rundunar 'yan sandan yace, "Wani mutum na tuka mota kirar Toyota sai ya hangi wata mata tana neman taimako.

"Sun tsaya sannan suka nemi taimakonta inda aka kwace motar a take. Daga bisani an rarrabe motar sannan aka siyar da ita. 'Yan sanda sun damke wadanda ake zargin daga bisani."

Nwabuzor ya kara da cewa, 'yan fashin sun saba kwace motocin jama'a ta wannan hanyar. A lokacin da aka tambaya matar, ta ce saurayinta ne ya ja ta.

KU KARANTA: Bidiyon jarumin da ya sha dambe da masu garkuwa da mutane, ya hana su satar jama'a da tsakar rana

'Yan sanda sun damke mace mai ciki wata 9 da wasu matasa 2 a kan fashi da makami
'Yan sanda sun damke mace mai ciki wata 9 da wasu matasa 2 a kan fashi da makami. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Ana musayar wuta tsakanin 'yan sanda da 'yan daba a wurin tattara sakamakon zabe

A wani labari na daban, rundunar dakarun sojin sama ta Operation Hadarin Daji ta halaka 'yan bindiga masu tarin yawa da ke yammacin Wagini ta jihar Katsina.

Kamar yadda hedkwatar tsaro ta Najeriya ta tabbatar, ta samu nasarar ragargaza sansanin wasu 'yan bindiga ne bayan bayanan sirrin da suka samu na wanzuwar wasu 'yan bindiga.

Shugaban fannin yada labarai na rundunar, Manjo Janar John Enenche, ya bayyana hakan a Abuja a ranar Asabar. Enenche ya ce sun aiwatar da samamen ne a ranar 8 ga watan Oktoba bayan bayanan sirri da suka samu wanda kuma suka tabbatar ta jiragen yaki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel