Shugaba Buhari ya kaiwa iyalan Yar'adua gaisuwar ta'aziyya a Kaduna (Hotuna)

Shugaba Buhari ya kaiwa iyalan Yar'adua gaisuwar ta'aziyya a Kaduna (Hotuna)

- Shugaba Buhari ya kai ziyara gidan iyalan marigayi Janar Shehu Musa Yar'adua

- Buhari ya kai gaisuwar ta'azziyar mutuwar Hajiya Rabi'atu

- Ya yi ziyaran tare da gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufa'i

Shugaba Muhammadu Buhari ya ziyarci iyalan Yar'adua bisa rasuwar Hajiya Rabi, surukar abokinsa, marigayi Janar Shehu Musa Yar'adua, a jihar Kaduna.

Buhari ya siffanta mutuwarta a matsayin babban rashi.

Shugaban kasa, wanda ya tafi Kaduna ranar Laraba domin halartan bikin yaye daliban jami'ar horar da Sojoji NDA, ya dauki lokaci domin ziyartar iyalan Yar'aduan a gidansu.

A jawabin da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, yayia Abuja, ya ce shugaba Buhari ya samu tarba daga wajen Hajiya Binta Yar'adua, matar marigayi Shehu Musa Yar'adua da diyar Hajiyar da ta rasu.

Buhari ya ce Hajiya Rabi ta yi rayuwa mai albarka kuma ta yi tasiri matuka kan wadanda sukayi rayuwa da ita.

Ya yi addu'a Allah ya karbi ibadunta.

KU KARANTA: Allah ya yiwa AbdulMalik, dan marigayi Sheikh Jafar Mahmoud Adam rasuwa

Shugaba Buhari ya kaiwa iyalan Yar'adua gaisuwar ta'aziyya a Kaduna (Hotuna)
Credit: @Buharisallau1
Asali: Twitter

DUBA NAN: Yan sanda sun damke tsohuwar da ta sayar da jikanta N1.3m saboda uban bai biya sadaki ba

Shugaba Buhari ya kaiwa iyalan Yar'adua gaisuwar ta'aziyya a Kaduna (Hotuna)
Credit: @Buharisallau1
Asali: Twitter

A wani labarin daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci taron yaye daliban jami'ar horar da Sojoji na 67 da Short Service 46 a jihar Kaduna ranar Asabar, 10 ga Oktoba, 2020.

A taron, shugaba BUhari ya gabatar da takobin girma ga zakaran dalibin shekar, Idris Olaiyan Salami.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel