An rasa rai guda yayin musayar wuta da 'yan sanda suka yi da 'yan fashi (Hotuna)

An rasa rai guda yayin musayar wuta da 'yan sanda suka yi da 'yan fashi (Hotuna)

- Jami'an 'yan sanda sun yi musayar wuta da wasu da ake zargin 'yan fashi da makami ne a jijhar Anambra

- Wadanda ake zargi 'yan fashin ne sun tare wani mota ne suna cikin yi wa 'yan cikin motar fashi amma aka sanar da 'yan sanda suka iso wurin

- Da isowarsu sai miyagun suka bude wuta hakan yasa suka fafata daga bisani 'yan sandan suka kashe daya daga cikinsu

An yi bata kashi tsakanin 'yan fashi da 'yan sanda a Anambra (Hotuna)
Bindigu da mota. Hoto daga @lindaikeji
Asali: Twitter

An kashe wani mutum guda sakamakon musayar wuta da 'yan sanda suka yi da gungun wasu da ake zargin 'yan fashi ne a Isiagu ring road da ke Awka, babban birnin jihar Anambra a ranar 9 ga watan Oktoba.

Sanarwar da kakakin 'yan sandan jihar Haruna Mohammed ya fitar ta ce an dade da sanin cewa wadanda ake zargin 'yan fashin ne suna adabar matafiya da ke bin hanyar.

DUBA WANNAN: Kiran dan majalisa dan luwadi, jahili a Facebook: Kotu ta tsare matashi a Gombe

"A ranar 9/10/2020 misalin karfe 9 an sanar da mu cewa wasu da ake zargin yan fashi ne sun tare Isiagu Ring road da ke karamar hukumar Akwa South suna yi wa wasu mutum uku da ke cikin mota bakar Accura Legend mai lamba SMK878GL fashi da bindiga.

"Isar jami'an 'yan sanda na SARS da 'yan banga na garin sai wadanda ake zargin 'yan fashin ne suka bude musu wuta suka yi watsi da fashin da suke yi.

An yi bata kashi tsakanin 'yan fashi da 'yan sanda a Anambra (Hotuna)
Bindigun da aka kwato daga hannun 'yan fashi. Hoto daga @lindaikeji
Asali: Twitter

"Yayin musayar wutan, an raunata daya daga cikin 'yan tawagar an kuma kwato bindiga daya da torch light da wayoyin salula uku a hannunsa da kudi. An garzaya da shi asibiti inda likita ya tabbatar ya mutu aka kai gawarsa dakin ajiye gawa.

KU KARANTA: Dattijo mai shekaru 106 ya auri sahibarsa mai shekaru 35 (Hotuna)

"Yan sandan sun datse dajin sun kuma sake nasarar gano wani bindiga da harsashi hudu. Ana cigaba da kokarin kamo wadanda ake zargin da ke neman tserewa da ake ganin an raunata su da harsashin bindiga," in ji sanarwar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel