Yan sanda sun damke tsohuwar da ta sayar da jikanta N1.3m saboda uban bai biya sadaki ba

Yan sanda sun damke tsohuwar da ta sayar da jikanta N1.3m saboda uban bai biya sadaki ba

- Wata tsohuwa ta shiga hannun jami'an tsaro kan laifin sayar da jikanta a kudi N1.3 million

- Tsohuwar mai suna Antonia Amos ta yi ikirarin cewa ta yi hakan ne saboda sirikinta ya ki biyan kudin sadakin 'yarta da ya aura

- Mahaifin yaran ne ya kai kara ofishin yan sanda kuma aka damketa

Jami'an yan sanda sun ceto wani jaririn makonni biyu da haihuwa a jihar RIvers bayan uwar mahaifiyarsa ta sayar da shi milyan 1.3.

Yan sanda sun bayyana cewa tsohuwar mai suna Antonia Amos ta sayar da yaron ne saboda mahaifinsa bai biya kudin sadakin auren mahaifiyar ('yarta) ba, Yabaleft ta ruwaito.

A cewar rahoton, an damke Antonia ne bayan mahaifin yaron, Christian Duru, ya kai kara ofishin yan sanda.

Kwamishanan yan sandan jihar, Joseph Mukan, ya ce Antonia ta kai yan sanda inda ta sayar da jaririn.

Da farko ta kai yan sandan karamar hukumar Ukanafun dake Akwa Ibom inda aka damke wata mata mai suna Pauline Umoh.

Sannan ta kaisu Mgbidi a jihar Imo wajen wacce ta sayi jaririn, Juliana Obianwa, inda aka kwato yaron kuma aka damketa.

A cewar Mukan, yan sanda na kokarin damke sauran mutane dake da hannu cikin wannan aika-aikan.

KU KARANTA: Abubuwa 7 da ya kamata ka sani game da zaben gwamnan jihar Ondo

Yan sanda sun damke kakar da ta sayar da jikanta N1.3m
Credit: Yabaleft
Asali: UGC

KU KARANTA: Buhari ya shiga ganawar sirri da IG na yan sanda kan zanga-zangan #ENDSARS

A wani labarin mai tashe, wani abin al'ajabi ya faru a jihar Legas, wata mata ta kara haihuwa bayan watanni 5 da haihuwar tagwaye.

Kamar yadda Enate Ogedegbe ya wallafa bikin sunan jariran a ranar Lahadi, 4 ga watan Oktoba, tare da wani Fasto Daniel Osierih, ya ce sai da matar tayi shekaru 7 da aure kafin ta samu haihuwar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel