Bidiyon yadda aka soka wa wani wuka a rumfar zabe a Ondo

Bidiyon yadda aka soka wa wani wuka a rumfar zabe a Ondo

- Mataimakin kwamishinan 'yan sandan jihar Ondo, ya tabbatar da yadda aka soka wa wani matashi wuka

- An soka wa matashin wuka ne yayin da suke wata rumfar zabe da ke cikin garin Akure na jihar Ondo

- Tuni matashin ya tashi kuma jami'an tsaro sun bazama neman 'yan daban da suka yi aika-aika

Wasu 'yan daba wadanda har yanzu ba a gano su waye ba, sun soka wa wani matashi wuka yayin da ake rumfar zabe a garin Akure da ke jihar Ondo.

Kamar yadda mataimakin kwamishinan 'yan sandan jihar ya tabbatar wa da Channels TV, matashin ya tashi kuma ya bayyana wa jami'an tsaro abinda ya faru.

Mataimakin kwamishinan 'yan sandan jihar, Lanre Bankole, ya ce ana kan bincike kuma za a bankado masu hannu a cikin aika-aikar.

KU KARANTA: Buhari ya sabunta nadin Faisal Shuaib a matsayin shugaban NPHCDA

KU KARANTA: Da duminsa: Daya daga cikin 'yan majalisar masarautar Zazzau ya yi murabus

A wani labari na daban, Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan yace za'ayi amfani da dokokin kare kai daga cutar COVID-19 a ranar Alhamis idan Buhari zai gabatar da kasafin kudaden 2021.

Yace da yawa daga cikin hadiman Buhari ba za su samu damar shiga majalisar ba. Duk wanda ke sha'awar ganin abubuwan da ke faruwa zai iya dubawa ta yanar gizo.

Duk da a shekarun baya gwamnoni, ministoci, shuwagabannin jam'iyyar APC da kuma hadiman Buhari na gaba-gaba wurin raka shi.

Bayan Lawan ya gama wannan jawabin ne sai sanatan Arewacin Kebbi, Yahaya Abdullahi ya gabatar da batun yadda 'yan majalisar wakilai zasu saurari bayani daga shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 8 ga watan Oktoba, 2020 da karfe 11 na safe akan kasafin kudaden 2021.

Shugaban majalisar dattawan yace za'ayi gabatarwar na tsawon awa 1. Kamar yadda yace, shugaban kasa zai yi bayani ne a majalisar wakilai.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel