Bidiyon ragargazar da dakarun soji suka yi wa 'yan bindiga a Katsina

Bidiyon ragargazar da dakarun soji suka yi wa 'yan bindiga a Katsina

- Dakarun sojin saman Operation Hadarin Daji sun ragargaza 'yan bindigar daji

- Hakan ta faru bayan samamen da sojin suka kai bayan bayanan sirrin da suka samu

- Maboyar 'yan ta'addan tare da wasu masu tarin yawa daga cikinsu sun halaka

Rundunar dakarun sojin sama ta Operation Hadarin Daji ta halaka 'yan bindiga masu tarin yawa da ke yammacin Wagini ta jihar Katsina.

Kamar yadda hedkwatar tsaro ta Najeriya ta tabbatar, ta samu nasarar ragargaza sansanin wasu 'yan bindiga ne bayan bayanan sirrin da suka samu na wanzuwar wasu 'yan bindiga.

Shugaban fannin yada labarai na rundunar, Manjo Janar John Enenche, ya bayyana hakan a Abuja a ranar Asabar.

Enenche ya ce sun aiwatar da samamen ne a ranar 8 ga watan Oktoba bayan bayanan sirri da suka samu wanda kuma suka tabbatar ta jiragen yaki.

A hakan aka hango 'yan bindiga tare da daruruwan shanu a sansaninsu.

Ya ce jiragen yakin sun ragargaji wurin inda suka tarwatsa sansanin tare da kashe da yawa daga cikin 'yan bindigar.

KU KARANTA: Makarfi ya yi martani a kan nadin Sarki Ahmed Bamalli Zazzau

Bidiyon ragargazar da dakarun soji suka yi wa 'yan bindiga a Katsina
Bidiyon ragargazar da dakarun soji suka yi wa 'yan bindiga a Katsina. Hoto daga @DefenceInfoNg
Asali: Twitter

KU KARANTA: Buhari ya sabunta nadin Faisal Shuaib a matsayin shugaban NPHCDA

A wani labari na daban, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo a ranar Talata, 6 ga watan Oktoba ya ce Najeriya tana da miliyoyin mutane da ke fama da matsanancin talauci.

Ya fadi hakan yayin da yake jawabi a wani taro a fadar shugaban kasa Abuja. Ya ce shugabannin da aka zaba basu da amfani indai har basu hada karfi da karfe wurin taimako a kan matsalar nan ba.

Ya ce, "Dole ne kowanne shugaba ya fahimci yadda zai tafiyar da mulkinsa. Idan aka kalli halin da miliyoyin talakawan Najeriya suke ciki, gashi yanzu cutar COVID-19 ta kara dagula komai, talauci da rashin aikin yi sun yawaita."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel