Zaben Ondo: Abubuwa 10 da ya dace ka sani game da dan takarar PDP, Eyitayo Jegede

Zaben Ondo: Abubuwa 10 da ya dace ka sani game da dan takarar PDP, Eyitayo Jegede

- Eyitayo Jegede, babban lauya mai mukamin SAN shine dan takarar jam'iyyar PDP a zaben gwamna na jihar Ondo na 2020

- Jegede ya taba rike mukamin attoney janar kuma kwamishinan shari'a na jihar Ondo babban dan siyasa ne a jihar

- A shekarar 2016, shine dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP kuma a yanzu ma jam'iyyar ta sake bashi tikitin takarar

Zaben Ondo: Abubuwa 10 da ya dace ka sani game da dan takarar PDP, Eyitayo Jegede
Etitayo Jegede (SAN). Hoto @TayoJegedeSAN
Asali: Twitter

Legit.ng ta kawo muku wasu muhimman abubuwa game da Jegede.

1. Sunan mahaifinsa Cif Johnson Jegede, Odopetu na Isinkan, Akure mahaifiyarsa kuma Misis C.O. Jegede daga garn Ipele kusa da Owo a jihar Ondo.

2. Ya yi karatun frimari a St. Stephen Primary School Modakeke, Ife sannan ya tafi Aquinas College daga Janairun 1973 zuwa 1978 inda ya yi kararun sakandare.

3. Shine kyaftin na kungiyar kwallon hannu na Volleyball a jami'ar Legas inda ya yi karatun lauya daga 1980 zuwa 1983.

DUBA WANNAN: Dattijo mai shekaru 106 ya auri sahibarsa mai shekaru 35 (Hotuna)

4. An tura shi jihar Adamawa don yin hidimar kasa wato NYSC inda a can ya fara koyan aikin lauya

5. A shekarar 1984, Jegede ya kammala karatun shekara 1 a makarantar horas da lauyoyi da ke Victoria Island, Legas kuma aka bashi lasisin fara aikin lauya 1984. Ya yi aiki a kamfanin lauyoyi na Murtala Aminu & Co Yola na shekaru 12.

6. Ya zama babban lauya mai mukamin SAN a 2008.

7. Ya taba rike mukamin shugaban kungiyar lauyoyi na Najeriya, NBA, reshen jihar Adamawa har sau biyu kuma shi mamba ne na Majalisar masu zartarwa na kungiyar da wasu kungiyoyin lauyoyi.

KU KARANTA: Zaben Ondo: Abubuwa 11 da ya dace ka sani game dan takarar jam'iyyar, APC Rotimi Akeredolu

8. Yana cikin kwamitin mutane biyar da aka daura wa nauyin kafa jami'ar Amurka ta Najeriya, (AUN) a jihar Adamawa.

9. Shi mamba na na Kwamitin Ilimin Lauya a Najeriya.

10. Shine tsohon mai kula kula da harkokin shari'a na cocin Anglican a Jalingo Jihar Taraba ya kuma taba rike mukamin a Yola.

A wani labrin daban, Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomi ta Najeriya, ALGON, ta tsige mataimakin ta na ƙasa Mohammed Aliyu Soba daga muƙaminsa.

Mr Soba shine shugaban ƙaramar hukumar Soba a jihar Kaduna kuma shugaban kungiyar reshen jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel