Zaben Ondo: Abubuwa 11 da ya dace ka sani game dan takarar jam'iyyar, APC Rotimi Akeredolu
- Gwamna Rotimi Akeredolu na daya daga cikin manyan 'yan takarar a zaben gwamnan jihar Ondo, ya lashe tikitin takarar APC a ranar Litinin 20 ga watan Yulin 2020
- Gwamnan mai ci a yanzu ya lashe zaben fidda gwani ja jam'iyyar bayan lashe kuri'u mafi yawa a dukkan kananan hukumomi 18 na jihar inda ya doke babban abokin karawarsa, Cif Oke da wasu 'yan takarar.
- A yayin da gwamnan ke neman yin tazarce, wasu 'yan takara ciki har da mataimakinsa, Agoola Ajayi na cikin masu son karbe kujerarsa

Asali: Twitter
Legit.ng ta kawo muku wasu muhimman abubuwa 11 game da dan takarar jam'iyyar APC a zaben gwamnan jihar Ondo na shekarar 2020.
1. Akeredolu ya fito ne daga karamar hukumar Owo a mazabar Ondo North.
2. An haife shi a ranar 21 ga watan Yulin 1956 a garin Owo, sunan mahaifinsa Reverend J. Ola Akeredolu mahaifiyarsa kuma Grace B. Akeredolu.
DUBA WANNAN: Dattijo mai shekaru 106 ya auri sahibarsa mai shekaru 35 (Hotuna)
3. Ya yi karatun frimari a makarantar gwamnati a garin Owo. Ya makarantun sakandare guda 3 wato Aquinas College, Akure, Loyola College, Ibadan da Comprehensive High School, Ayetoro.
4. Ya kuma yi digiri a fanin lauya a Jami'ar Ife (yanzu Jami'ar Obafemi Awolowo).
5. Ya samu lasisin fara aikin lauya a 1978 kuma ya zama SAN a 1988.
6. An nada shi attoney janar na jihar Ondo daga 1997 zuwa 1999.
7. A shekarar 2008, ya yi aiki a matsayin shugaban kungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA).
KU KARANTA: Kiran dan majalisa dan luwadi, jahili a Facebook: Kotu ta tsare matashi a Gombe
8. Akeredolu na cikin masu kula da kamfanin aikin lauya na Olujinmi & Akeredolu da suka kafa tare da Cif Akin Olujinmi tsohon attoney janar kuma ministan shari'a na Najeriya.
9. Akeredolu ya yi takarar gwamna a karkashin jam'iyyar Action Congress of Nigeria (ACN) a zaben 2013.
10. An zabe shi gwamna a karo na farko a shekarar 2016 bayan ya kada dan takarar jam'iyyar PDP, Etitayo Jegede.
11. Yana auren Betty Anywanwu-Akeredolu 'yar asalin jihar Imo. Sun hadu wurin yi wa kasa hidima NYSC kuma suna da yara hudu.
A wani labrin daban, Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomi ta Najeriya, ALGON, ta tsige mataimakin ta na ƙasa Mohammed Aliyu Soba daga muƙaminsa.
Mr Soba shine shugaban ƙaramar hukumar Soba a jihar Kaduna kuma shugaban kungiyar reshen jihar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng