Bidiyon jarumin da ya sha dambe da masu garkuwa da mutane, ya hana su satar jama'a da tsakar rana

Bidiyon jarumin da ya sha dambe da masu garkuwa da mutane, ya hana su satar jama'a da tsakar rana

- Wani bidiyo mai matukar firgici ya karade kafafen sada zumuntar zamani inda ake kokarin yin garkuwa da mutane da tsakar rana

- Amma kuma, wani jarumin maza da ke inda abun ke faruwa ya gaggauta daukar matakin hana garkuwar da mutane

- Bidiyon ya karade kafafen sada zumuntar zamani kuma mazauna kasar Afrika ta kudu sun dinga cece-kuce

Jama'a da yawa kan zauna su zuba ido ko kuma su nemi wurin boyewa matukar ana aikata laifi saboda tsoron kada ya shafesu.

Duk da bai wa kai kariya ba abu ne mara kyau ba, kawai yana nuna yadda jama'a ke mutunta rayuwarsu ne da gudun ta subuce musu.

Amma kuma, akwai jama'a da suka kasance jarumai wadanda saboda kokarinsu basu iya zuba ido su ga ana cutar da wasu.

Wani bidiyo mai matukar firgitarwa ya fada kafafen sada zumuntar zamani inda 'yan daba ke kokarin garkuwa da wata yarinya da rana tsaka yayin da take cin abinci da mahaifiyarta.

Amma kuma cike da sa'a, wani mutum ya bayyana a take sannan ya dauka mataki. Ya hana masu garkuwa da mutanen daukar yarinyar.

Kamar yadda Yusuf Abramjee ya bayyana, lamarin ya faru a wani wuri ne da ake kira da Bella Napoli, Goldman Crossin, Florida, West Rand.

Jarumtar bawan Allah ya sa har jami'an tsaro sun iso sannan suka cafke mmasu garkuwa da mutanen.

KU KARANTA: Da duminsa: Daya daga cikin 'yan majalisar masarautar Zazzau ya yi murabus

Bidiyon jarumin da ya sha dambe da masu garkuwa da mutane, ya hana su satar jama'a da tsakar rana
Bidiyon jarumin da ya sha dambe da masu garkuwa da mutane, ya hana su satar jama'a da tsakar rana. Hoto daga @GavinCarter83
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hotuna: Munir Jaafaru ya kai wa sabon Sarki ziyara, ya yi mubaya'a

A wani labari na daban, Elisha Abbo, Sanata mai wakiltar mazabar Adamawa ta arewa, ya daukaka kara inda yake kalubalantar hukuncin wata babbar kotun tarayya wacce ta ci tararsa naira miliyan 50 a kan cin zarafin wata mata.

A 2019, 'yan sanda sun gurfanar da Abbo a gaban wata kotun majistare da ke Zuba, a kan zarginsa da laifin cin zarafin wata mata mai suna Osimibibra Warmate a wani shago a Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel