Yanzu-yanzu: Mutane 151 suka kamu da cutar Korona Juma'a, jimilla 55,992

Yanzu-yanzu: Mutane 151 suka kamu da cutar Korona Juma'a, jimilla 55,992

Hukumar hana Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar COVID-19 ta sake harbin sabbin mutane 151 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:15 na daren ranar Juma'a 9 ga watan Oktoba, shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta fitar, ta ce mutanen 151 sun fito daga jihohin Najeriya kamar haka:

Lagos-71

Ogun-26

Kaduna-17

Osun-10

Oyo-8

FCT-6

Rivers-6

Plateau-5

Akwa Ibom-1

Ekiti-1

DUBA NAN: Buhari ya shiga ganawar sirri da IG na yan sanda kan zanga-zangan #ENDSARS

Kawo yanzu a duk fadin Najeriya, cutar ta harbi mutum 59,992, sai kuma mutum 51,614 da aka sallama daga cibiyoyin killace masu cutar bayan samun waraka, yayin da mutum 1113 suka riga mu gidan gaskiya.

KARANTA WANNAN: Najeriya fa kamar mota ce mara matuki (direba) - Attahiru Jega da sauran manya

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel