Yanzu-yanzu: Buhari ya shiga ganawar sirri da IG na yan sanda kan zanga-zangan #ENDSARS

Yanzu-yanzu: Buhari ya shiga ganawar sirri da IG na yan sanda kan zanga-zangan #ENDSARS

- Karo na biyu cikin rana daya, Buhari ya gana da sifeto janar na yan sanda

- Yan Najeriya a Legas, Abuja, Oyo, Osun, Delta dss suna zanga-zanga kan zaluncin yan sandan SARS

- Jami'an SARS sun yi kaurin suna da cin zarafin matasa a kudancin Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari ya sake shiga wani ganawa da sifeto janar na yan sanda, IGP Mohammed Adamu da daren nan zanga-zangan da matasa ke yi na kuka da jami'an yan sandan SARS.

A wannan karon, an yi zaman da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.

Shugaban kasan da kansa ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita inda ya baiwa IG Adamu umurnin daukan matakin da ya dace wajen kawo karshen cin zarafin matasan da yan sanda ke yi.

Buhari ya yi kira da yan Najeriya su kara hakuri ko da zasu gudanar da zanga-zanga saboda hakan hakkinsu ne.

DUBA NAN: Najeriya fa kamar mota ce mara matuki (direba) - Attahiru Jega da sauran manya

"Na sake ganawa da IGP da daren nan. Manufarmu itace gyara hukumar yan sanda. Ina samun bayanai akai-akai kan kokarin da akeyi na gyara domin kawo karshen cin zarafi da yan sanda ke yi da ayyukan assha." Buhari yace

"Nai baiwa IG umurnin shawo kan korafe-korafen yan Najeriya game da cin zarafi da kuma tabbatar da cewa an hukunta jami'an yan sandan da sukayi ba daidai ba."

"Ina kira ga yan Najeriya suyi hakuri."

Yanzu-yanzu: Buhari ya shiga ganawar sirri da IG na yan sanda kan zanga-zangan #ENDSARS
Hoton Buhari bayan ganawar Credit: @MBuhari
Asali: Twitter

KU KARANTA: Barawo ya fasa cikin majalisar wakilai, ya kwashe daloli da kayayyaki

Mun kawo muku rahoton cewa Frank Mba, mai magana da yawun rundunar ƴan-sanda, ya ce abune mawuyaci ƙungiyar da ta san abun da take yi ta nemi a kawo ƙarshen sashen hana fashi da makami (SARS).

Da yake magana game da zanga-zangar da ake gudanarwa a kan neman rushe sashen hana fashi da makami na rundunar yan sanda, Mba yace wasu daga cikin jami'an su na daga cikin masu yaƙi da ta'addanci da kuma fashi a Arewacin Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel