Abubuwa 7 da ya kamata ka sani game da zaben gwamnan jihar Ondo

Abubuwa 7 da ya kamata ka sani game da zaben gwamnan jihar Ondo

Shirye-shirye na cigaba da gudana na zaben gwamnan jihar Ondo da hukumar zabe ta kasa watau INEC ta shirya ranar Asabar, 10 ga watan Oktoba, 2020.

Tuni hukumar ta fara raba kayayyakin zabe masu muhimmanci irinsu na'urar tantance masu zabe wanda akafi sani da 'Card Reader, takardun kuri'a da akwatunan zabe zuwa dukkan lunguna da sakon jihar Ondo.

Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu, tare da shugabannin kwamitin zaman lafiya ta kasa karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa, AbdulSalam Abubakar, sun tabbatar da cewa dukkan yan takara sun rattafa hannu kan takardan alkawarin cewa ba zasu yi rigima ba.

Abubuwa 7 da ya kamata ka sani game da zaben gwamnan jihar Ondo da za'ayi gobe Asabar
Abubuwa 7 da ya kamata ka sani game da zaben gwamnan jihar Ondo da za'ayi gobe Asabar
Asali: UGC

KU KARANTA: Mako daya da bude Masallacin Harama, mutane 24,000 sun yi ibadar Umarah

Legit Hausa ta kawo muku sharhin abubuwa bakwai da ya kamata ku sani game da zaben gwamnan kamar yadda taswirar TheCableIndex ya nuna:

1. Adadin yan takara: Yan takara 17 zasu kara a zaben gobe. Yayinda 16 maza ne, akwai mace guda daya kacal

2. Adadin kananan hukumomin da za'ayi zabe a jihar: Akwai kananan hukumomin 18 a jihar Ondo kuma ana kan tura kayayyakin zabe yanzu haka, kamar yadda INEC ta bayyana.

Kananan hukumomin sune Akoko North-East, Akoko North-West, Akoko South-East, Akoko South-West, Akure North, Akure South, Ese Odo, Idanre, Ifedore, Ilaje , da Ile Oluji/Okeigbo.

Sauran sune, Irele , Odigbo , Okitipupa, Ondo East, Ondo West, Ose da Owo.

DUBA NAN: Najeriya fa kamar mota ce mara matuki (direba) - Attahiru Jega da sauran manya

3. Adadin gundumam dake jihar: Akwai gunduma-gunduma 203 a fadin jihar Ondo

4. Adadin rumfunan zabe. Akwai rumfar zaben 3009

5. Adadin mutanen da ake kyautata zaton zasu kada kuria: Mutane 1,478,460 suka karbi katin zabensu.

6. Adadin katin zaben da ba'a karba ba: Kimanin mutane 343,886 basu karbi ktin zabensu ba kuma ba zasu iya kada kuri'a ba.

7. Su waye manyan yan takara?: Akwai manyan yan takara uku cikin yan takara 17, sune:

Oluwarotimi Akeredolu SAN - Jam'iyyar APC

Eyitayo Jegede SAN - Jam'iyyar PDP

Agboola Ajayi - Jam'iyyar ZLP

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel