PSC ta kori ACP da sauran wasu manyan jami'an 'yan sanda 9

PSC ta kori ACP da sauran wasu manyan jami'an 'yan sanda 9

- Hukumar kula da 'yan sanda (PSC) ta dauki mataki a kan wasu manyan jami'an 'yan sanda da aka gurfanar gabanta

- Ana zargin manyan jami'an da aikata laifuka daban-daban da su ka saba da dokoki da tsarin aikin dan sanda

Hukumar kula da rundunar 'yan sanda (PSC) ta amince da korar manyan jami'an 'yan sanda 10 tare da ragewa wasu 9 mukami.

Kazalika PSC ta amince da shawarar zartar da hukunci mai tsanani a kan wasu jami'ai 8 tare da bawa wasu jami'ai uku takardar gargadi.

Hukumar ta wanke wasu jami'ai uku da ake zargi da aikata laifi a yayin da ta amince da dakatar da albashin wasu jami'ai 10 a matsayin horo.

Hakan na kunshe ne a cikin wani jawabi da Ikechukwu Ani, shugaban sashen yada labarai da hulda da jama'a a PSC, ya fitar ranar Juma'a.

"PSC ta yanke wadannan shawarwari ne yayin zaman darektocinta, wanda aka yi ranar Talata, 28 ga watan Satumba, a Abuja karkashin jagorancin ciyaman, Musliu Smith, tsohon sifeton rundunar 'yan sanda.

KARANTA: An kashe dan sanda; zanga-zangar neman rushe SARS ta rikide zuwa rikici a wasu jihohi 3

"Yayin zaman, an tattauna a kan tuhumar zargin aikata laifuka da ake yi wa jami'ai 43.

"Daga cikinsu, PSC ta amince da korar wani mataimakin kwamishina (ACP), jami'ai biyu ma su mukamin SP, jami'ai uku ma su mukamin DSP da kuma jami'ai hudu ma su mukamin ASP.

PSC ta kori ACP da sauran wasu manyan jami'an 'yan sanda 9
IGP Mohammed Adamu
Asali: UGC

"Kazalika, PSC ta bayar da umarnin gurfanar da wasu manyan jami'ai 6 da suka hada da; ACP , SP, DSPs biyu, da ASPs biyu," a cewarsa.

KARANTA: Sojoji sun yi 'caraf' da mai safarar makamai ga kungiyar Boko Haram daga ketare

Ya bayyana sunayen jami'an da abinda ya shafa kamar haka; jami'an 10 da aka kora, ACP Magaji Ado Doko, SP Ogedengbe Abraham, SP Mallam Gajere Taluwai, DSP Okunkonin Daniel, DSP Abisoro Obo Irene, DSP Theresa Nuhu (mai ritaya).

Sai ASP Sanusi Rasaki, ASP Uwadala Ehis Oba, ASP Ferdinand Idoko, da ASP Igolor Godsent Ogheneruona.

Jami'an da aka ragewa mukami sune kamar haka; Muhammad Sani Muhammad daga CSP zuwa SP, John Oluwarotimi daga SP zuwa DSP.

Sai Godwin Agbo da Hassan Hamidu daga DSP zuwa ASP da kuma Edeke Michael da Iyanda Olufemi wadanda aka ragewa mukami zuwa Insifekta daga ASP.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayarku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng