Rundunar soji ta salwantar da ran wani shugaban 'yan bindiga a Filato

Rundunar soji ta salwantar da ran wani shugaban 'yan bindiga a Filato

- Rundunar sojoji na cigaba da samun nasarorin ragargazar 'yan ta'adda a jihohi daban-daban

- A ranar Alhamis rundunar OPSH sun kashe shugaban 'yan ta'addan kauyen Tafawa dake jihar Plateau

- Duk da ya samu ya tsere kwanakin baya, bayan sojojin sun ji masa munanan raunuka

A ranar Alhamis, rundunar OPSH ta samu nasarar kashe shugaban 'yan bindiga dake kauyen Tafawa a karamar hukumar Barikin Ladi a jihar Plateau, Daily Trust ta wallafa.

Manjo Janar John Enenche, kakakin rundunar soji, ya sanar da hakan a wata takarda, inda ya sanar da ragargazar 'yan ta'adda da suka samu nasarar yi.

"A 'yan kwanakin nan, rundunar soji sun samu nasarori sakamakon amfani da dabaru masu dumbin yawa wurin ragargazar 'yan ta'adda.

"A ranar 26 ga watan Satumba, 2020, rundunar Operation SAFE HAVEN sun ragargaji 'yan ta'adda a Bisichi.

"A lokacin ne rundunar ta ji wa shugaban 'yan ta'addan munanan ciwuka, amma ya samu ya tsare, inda aka yi ta kula da lafiyarsa a wata maboyarsu dake kauyen Tafawa," kamar yadda takardar ta zo.

KU KARANTA: Ahmed Lawan ya shawarci Buhari da ya guji cin bashi don aiwatar da manyan ayyuka

Rundunar soji ta salwantar da ran wani shugaban 'yan bindiga a Filato
Rundunar soji ta salwantar da ran wani shugaban 'yan bindiga a Filato. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan majalisar nadin sarakuna 5 sun yi wa Bamalli mubaya'a

A wani labari na daban, hedkwatar tsaro tace rundunar sojin sama ta 'Operation Thunder Strike' ta ragargaji wata maboyar 'yan bindiga, inda ta samu nasarar kashesu a daji da kuma jihohi masu iyakoki da jihar Kaduna.

Shugaban fannin yada labarai, Manjo Janar John Enenche ya sanar da hakan a wata takarda ta ranar Alhamis a Abuja, yace wannan sabon shiri ne na rundunar sama ta "Operation Kashe Mugu 2".

Enenche yace rundunar tayi harbin a dajin Kuyambana, Fadaman Kanauta da Jan-Birni a ranar 6 da 7 ga watan Oktoba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel