Babu jihar da ta kai Kano yaki da rashawa a kasar nan - Ganduje

Babu jihar da ta kai Kano yaki da rashawa a kasar nan - Ganduje

- Gwamnatin jihar Kano ta yi ikirarin cewa itace jagorar yaki da rashawa a Najeriya

- Gwamnan jihar ya bayyana cewa jihar ta kafa makarantar koyar da ilimin yaki da rashawa

- Hukumomin yaki da rashawa da kare hakkin dan Adam sun jinjinawa Kano

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce babu jihar da ta kai jiharsa yaki da rashawa a Najeriya saboda jihar kadai ke da hukumar mai karfi a gaba daya kasar mai kokari.

Ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a taron murnar ranar Ombudsman da akayi a makarantar yaki da rashawa (KANCI) a Kano, Daily Trust ta ruwaito.

Ganduje wanda ya samu wakilcin kwamishanan shari'ar jihar, Barista Lawan Musa Abdullahi, ya ce kafa hukumar korafe-korafe da yaki da rashawa PCACC da kuma makarantar yaki da rashawa ya nuna cewa jihar na kokarinta wajen taimakawa gwamnatin tarayya wajen yaki da rashawa.

A cewar shugaban hukumar, Muhuyi Mahaji Rimin Gado, ya ce dokar jihar da ta kafa hukumar ta bata daman hukunta duk wanda aka samu da kashi a gindi.

Ya ce karkashin sashe na 9 na dokar, PCACC na da hakkin tabbatar da cewa ba'a cuci dan jihar Kano ba.

Wakilan hukumomin EFCC, ICPC da NHRC sun jinjinawa kokarin hukumar wajen hadin kan da take badawa wajen yaki da rashawa.

KU KARANTA: An yi zaman majalisar Sarki na farko karkashin Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli (Hotuna)

Babu jihar da ta kai Kano yaki da rashawa a kasar nan - Ganduje
Credit: @dawisu
Asali: Twitter

DUBA NAN: Sojoji sun yi 'caraf' da mai safarar makamai ga kungiyar Boko Haram daga ketare

A wani labarin daban, gwamnatin jihar Kano ta sahale gina manyan makarantun haɗaka guda biyar a masarautun jihar daban-daban. Makarantu zasu fara aiki ne daga zangon karatu na shekarar 2021/2022.

Kwamishinan ilimi na jihar kano Malam Muhammad Sunusi Sa'id Ƙiru,yace kowacce masarauta zata rabauta da makarantar haɗaka guda ɗaya.

A bayanan da jami'in hulɗa da jama'a na ma'aikatar ilmi, Aliyu Yusuf, ya fitar yac e wannan shawarar na daga cikin matsaya da majalisar zartawar jihar ta cimma a taron da ta gudanar ranar Talata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel