EndSars: Masu zanga-zanga sun kashe dan sanda, sun raunata wani sun kuma sace AK47

EndSars: Masu zanga-zanga sun kashe dan sanda, sun raunata wani sun kuma sace AK47

- IGP na 'yan sandan Najeriya ya yi tir da kisar da wasu masu zanga-zanga suka yi wa jami'in dan sanda a jihar Delta

- IG Adamu ya yi gargadin cewa rundunar 'yan sanda ba za ta amince wasu da ke ikirarin zanga-zanga su sake kashe wani jami'in tsaro ba

- Shugaban 'yan sandan ya ce al'umma na da ikon yin zanga-zangan lumana amma dole ayi shi bisa yadda doka ta tanada

Sufeta Janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya yi Allah wadai da harin da masu zanga-zangar #ENDSARS suka kai wa 'yan sanda a Ughelli jihar Delta a ranar 8 ga watan Oktoba.

Matasa a Ughelli sun fito kwansu da kwarkwata sun yi zanga-zanga na neman a soke rundunar 'yan sanda ta musamman masu yaki da 'yan fashi wato SARS.

DUBA WANNAN: An cafke masu yi wa Boko Haram jigilar man fetur a Borno

EndSars: Masu zanga-zanga sun kashe dan sanda, sun raunata wani sun kuma sace AK47
IGP Mohammed Adamu. Hoto: @DailyPostNGR
Asali: Twitter

Sanarwar da kakakin 'yan sandan Najeriya, DCP Frank Mba ya fitar ya ce masu zanga-zangar sun kashe wani Kofur Etaga Stanley a Ugelli kuma sun raunta wani jami'in, Saja Patrick Okuone.

"Masu zanga-zangar sunyi awon gaba da AK 47 guda daya mai lamba 56-2609008 da harsasai 25 da ke tare da marigayin a lokacin da abin ya faru," a cewar sanarwar Mba.

Sufetan 'yan sandan da ya bayyana harin a matsayin zalunci ya yi gargadin cewa rundunar ba za ta lamunci hari a kan jami'anta ba ko wani jami'in tsaro daga wasu da ke ikirarin yin zanga-zanga.

KU KARANTA: Dattijo mai shekaru 106 ya auri sahibarsa mai shekaru 35 (Hotuna)

IGP din ya ce 'yan kasa na da damar yin zanga-zanga na lumana amma ya zama dole ayi shi cikin tsari da kiyaye dokokin kasa.

Shugaban 'yan sandan ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan marigayi Kofur Etaga Stanley sannan ya jinjinawa rundunar 'yan sandan ta jihar Delta saboda kame kai da ta yi yayin harin da aka kai mata.

IGP ya umurci kwamishinan 'yan sanda na jihar Delta ya gudanar da bincike kan lamarin a gano wadanda ke da hannu a kuma gurfanar da su gaban kuliya.

A wani labarin, daban, wani dan gidan haya mai shekara 21 Onyemachi Mmaju, ya kashe mai gidan hayar da ya ke zama, Nonso Oyiboko a garin Ogidi a karamar hukumar Idemili na jihar Anambra. The Punch ta ruwaito cewa an fara samun rashin jituwa tsakanin mai gidan da dan hayan ne bayan Oyiboka ya koka kan yadda Mnaju ke kawo 'yan mata gidan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel