An kashe jami'in NDLEA a Adamawa bayan masu safarar kwayoyi sun masa sharrin ya yi garkuwa da su

An kashe jami'in NDLEA a Adamawa bayan masu safarar kwayoyi sun masa sharrin ya yi garkuwa da su

- Wasu masu safarar kwayoyi sun yi wa jami'an NDLEA sharrin cewa sunyi garkuwa da su hakan yasa mutane suka afka musu da suka

- Fusatattun matasa da suka afka wa jami'an na NDLEA sun kashe guda daya sun kuma raunta guda

- Lamarin ya faru ne a jihar Adamawa a lokacin da jami'an na NDLEA suka kamo masu safarar kwayoyi za su tafi dasu Yola

Wani jami'in hukumar yaki da masu ta'amulli da miyagun kwayoyi na kasa (NDLEA) Samuel Birma ya rasa ransa sakamakon duka da aka masa a Adamawa bayan da masu safarar kwayoyi suka masa sharrin ya yi garkuwa da su.

An ruwaito cewa Birma da abokan aikinsa sun kamo wasu da ake zargin masu safarar miyagun kwayoyi ne a Michika za su kai su Yola yayinda matasan suka kai musu hari.

An kashe jami'in NDLEA a Adamawa bayan masu safarar kwayoyi sun masa sharri
Samuel Birma. Hoto: Abba Monday
Asali: Facebook

Masu safarar kwayoyin da aka kamo sun tunzura matasar inda suka yi ikirarin cewa garkuwa da su aka yi nan take aka afka wa jami'an NDLEA da duka inda aka kashe Birma aka raunata abokin aikinsa.

Marigayi Birma da aka fi sani da Mbakwe dan asalin garin Hildi ne daga karamar hukumar Hong na jihar Adamawa.

"Da isarsu wurin da ya ke ranar cin kasuwa ne, wadanda ake zargin suka yi ihun cewa an sato su ne kuma suka nemi taimako, hakan yasa mutane suka kai musu dauki," kamar yadda wata majiya ta shaida wa Premium Times.

"Jami'an na NDLEA sunyi kokarin nuna wa mutane katin shaidan aikinsu amma mutanen ba su kula su ba suka afka musu da duka da hari da muggan makamai suka kashe daya daga ciki suka kona gawarsa yayinda dayan ya jikkata sosai," a cewar majiyar.

Kakakin 'yan sandan jihar Adamawa, DSP Suleiman Nguroje ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Alhamis 8 ga watan Oktoba ya ce an fara bincike don gano ainihin abinda ya faru.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel