Jerin al'adu 3 da ake tabbatarwa kafin sabon Sarki a Zazzau ya shiga fadarsa

Jerin al'adu 3 da ake tabbatarwa kafin sabon Sarki a Zazzau ya shiga fadarsa

- Bayan rasuwar Sarkin Zazzau, gwamnatin jihar Kaduna ta nada Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sarkin Zazzau

- Yayan sarkin, Alhaji Aliyu Nuhu Bamalli a hirarsa da aka yi da shi, ya sanar da yadda ake gudanar da nadin sarautar Zazzau

- Yayan Sarkin, wanda yanzu haka yake rike da sarautar Zumar Zazzau ya sanar da abubuwa 3 da wajibi ne ayi su a bikin nadin sarki

Bayan rasuwar Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris a ranar 20 ga watan Satumba 2020, gwamnatin jihar Kaduna ta nada Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli.

Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli jakaden Najeriya ne a Thailand, kuma Magajin Garin Zazzau kafin a nada sa a matsayin sarkin Zazzau.

Mahaifinsa, Nuhu Bamalli, tsohon minista ne a Najeriya, ya rasu a 2001.

A tattaunawar BBC da yayan sarkin, Alhaji Aliyu Nuhu Bamalli wato Zuman Zazzau, ya sanar da al'adu 3 da ake yi kafin sabon Sarki ya shiga fadarsa.

1. 'Yan majalisar sarki zasu yi mubaya'a

Kamar yadda Zuman Zazzau ya ce, 'yan majalisar sarki suna mubaya'a ne bayan nadin sabon sarki.

Kamar yadda yazo a al'ada, 'yan majalisar sarki za su kai wa sabon Sarki gaisuwa suna yi masa maraba.

2. Sabon sarki ba zai yi zaman fada ba har sai anyi masa nadi.

Kamar yadda Zumar Zazzau ya shaida, wajibi ne ayi bikin nadin sabon sarkin, fadawa su raka shi fada, sannan ya hau karagar mulki idan ya amshi sandar sarki.

3. Wajibi ne yin nadin sarauta a Zaria

Alhaji Aliyu Nuhu Bamalli ya ce al'adar Zazzau ta bambanta da yadda ake yi a wasu masarautun.

Ya ce, "A masarautar Zazzau, wajibi ne yin bikin nadi a Zaria, ba babban birnin jihar Kaduna ba. Gwamna da sauran baki za su zo masarauta domin gudanar da shagalin bikin nadin sarkin."

KU KARANTA: Najeriya tana da miliyoyin jama'a da ke fama da tsananin talauci - Osinbajo

Jerin al'adu 3 da ake tabbatarwa kafin sabon Sarki a Zazzau ya shiga fadarsa
Jerin al'adu 3 da ake tabbatarwa kafin sabon Sarki a Zazzau ya shiga fadarsa. Hoto daga @GovKaduna
Asali: UGC

KU KARANTA: NASS ta hana wasu hadimai da ministocin Buhari rakiyar gabatar da kasafin kudi

A wani labari na daban, daya daga cikin manema sarautar Zazzau, Munir Ja'afaru ya ziyarci sabon Sarki, Ahmed Nuhu Bamalli, a fadarsa da ke cikin Zaria, jihar Kaduna.

Idan ba'a manta ba, a ranar Laraba, Gwamna Nasir El-Rufai ya nada Nuhu Bamalli a matsayin sarkin Zazzau, bayan rasuwar Sarki Shehu Idris a ranar Lahadi, 20 ga watan Satumba, bayan mulkar Zazzau na tsawon shekaru 45.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel