Dakarun soji sama sun ragargaji 'yan bindigar daji a Kaduna

Dakarun soji sama sun ragargaji 'yan bindigar daji a Kaduna

- Hedkwatar tsaro ta kara sanar da nasarar ragargazar maboyar 'yan ta'adda a jihar Kaduna

- Rundunar tayi amfani da ISR don gano bukkokin 'yan bindigar a dajin Kuyambana

- Bayan gano bukkokinsu, sun yi ta ragargazarsu da makamansu ta sama

Hedkwatar tsaro tace rundunar sojin sama ta 'Operation Thunder Strike' ta ragargaji wata maboyar 'yan bindiga, inda ta samu nasarar kashesu a daji da kuma jihohi masu iyakoki da jihar Kaduna.

Shugaban fannin yada labarai, Manjo Janar John Enenche ya sanar da hakan a wata takarda ta ranar Alhamis a Abuja, yace wannan sabon shiri ne na rundunar sama ta "Operation Kashe Mugu 2".

Enenche yace rundunar tayi harbin a dajin Kuyambana, Fadaman Kanauta da Jan-Birni a ranar 6 da 7 ga watan Oktoba.

Yayi bayanin yadda ISR suka gano cewa 'yan bindigar suna amfani da dazuzzukan don garkuwa da mutane, adana makamai, kai hari da kuma adana shanu.

Yace an kai wa 'yan bindigar hari ne bayan ISR sun gano bukkoki 4 inda 'yan ta'addan suka yada zango.

Jiragen rundunar NAF sun yi dacen harbin daidai bukkokin 'yan ta'addan, har suka samu nasarar kama wasu 'yan ta'adda.

Jiragen NAF sun yi nasarar yin kaca-kaca da 'yan ta'addan Fadaman Kanauta da na Jan-Birni, har da lalata masu maboyar su.

Ya ce, "Rundunar sojin Najeriya na mika sakon gaisuwa da kuma godiya maras adadi ga 'yan Najeriya sakamakon taimako da labaran da zasu taimaka wurin gano inda 'yan ta'adda ke boyewa don samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya."

KU KARANTA: Akwai yuwuwar maza masu babbar murya su fi sauran maza iya cin amana - Sabon bincike

Dakarun soji sama sun ragargaji 'yan bindigar daji a Kaduna
Dakarun soji sama sun ragargaji 'yan bindigar daji a Kaduna. Hoto daga @Dailynigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Masu zanga-zanga sun yi wa hedkwatar 'yan sanda zobe a Abuja

A wani labari na daban, bayan nadin sabon sarkin Zazzau, an tsananta tsaro a farfajiyar fadar sabon Sarkin Zazzau. Gidan talabijin na Channels sun nuna yadda mutane suka yi ta kutsawa fadar suna murna.

Al'amarin ya biyo bayan nada Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sarkin Zazzau na 19 wanda Gwamna Nasir El-Rufai yayi.

Bamalli ya gaji marigayi sarki Shehu Idris wanda ya rasu a ranar 20 ga watan Satumba, 2020 bayan mulkar masarautar na shekaru 45.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel