Dattijo mai shekaru 106 ya auri sahibarsa mai shekaru 35 (Hotuna)

Dattijo mai shekaru 106 ya auri sahibarsa mai shekaru 35 (Hotuna)

- An daura auren wani dattijo mai shekaru 106 da matarsa mai shekaru 35 a yankin yammacin kasar Ghana

- Dattijon ya hadu da matar ne bayan rasuwar matarsa na farko tun shekarar 1999 ama suke zaune ba aure

- Dansa ya ce dattijon ya bukaci a daura auren ne don yana tsoron idan ya mutu Ubangiji ya tambaye shi dalilinsa na kin auren matar

Hotuna: Dattijo mai shekaru 106 ya auri sahibarsa mai shekaru 35
Ma'aurata daga Ghana. Hoto: @lindaikeji
Asali: Instagram

Wasu sabbin ma'aurata sun yi fice a dandalin sada zumunta bayan da hotunan daurin auren su ya bazu a shafun yanar gizo.

Hoton na dauke da dattijo da aka ce shekarunsa 106 da matarsa mai shekara 35 a yayin bikin daurin aurensu na gargajiya.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa 'yan daba suka tube wa Fayose hula a Ondo

A cikin hotunan da suka karade dandalin sada zumunta na yara gizo, ana iya ganin angon da amaryarsa sanye da kente suna cashewa.

Ga shi sun rike hannun juna yayin da suka kewaye da taron al'umma na 'yan uwa da abokan arziki da suka zo shaida auren.

Adom TV ta ruwaito cewa an yi bikin auren ne a Maafo-Akwaboakrom da ke yankin yammacin Ghana.

A cewar Gyan Formula, wani mutum da ya ce mahaifinsa ne angon ya ce shekarun mahaifin 106 sannan shekarun matar 35.

Gyan ya ce sun yi kimanin shekaru 12 suna zama tare kuma suna da yara 12 babban cikinsu dan shekara 11 ne.

Gyan ya ce mahaifinsa manomin cocoa ne kuma mai bada maganin gargajiya sannan yana da karfinsa.

KARANTA NAN: An cafke masu yi wa Boko Haram jigilar man fetur a Borno

Da ya ke bayani kan dalilin da yasa mahaifinsa ya yi auren yanzu ya ce yana fargabar mutuwa ne ba tare da ya auri matar ba kuma Ubangiji ya masa tambaya a kan hakan.

Da ya ke tsokaci kan dangantakarsu, Gyan mai shekaru 41 ya ce shi da sauran 'yan uwansa sun dauke ta tamkar uwa.

A cewarsa, mahaifiyarsu ta rasu a 1999 kuma sun amince da matar saboda mahaifinsu yana kaunar ta kuma tana faranta masa rai.

Ga hotunan ma'auratan a kasa:

Hotuna: Dattijo mai shekaru 106 ya auri sahibarsa mai shekaru 35
Ma'aurata daga Ghana: Hoto: @lindaikeji
Asali: Instagram

Hotuna: Dattijo mai shekaru 106 ya auri sahibarsa mai shekaru 35
Ma'aurata daga Ghana. Hoto: @lindaikeji
Asali: Instagram

A wani labarin, Jam'iyyar PDP ta ce bata amince da nada shugaban jami'ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife, Farfesa Etiyope Ogunbodede a matsayin baturen zabe na zaben gwamna da za ayi ranar Asabar a jihar Ondo ba.

Shugaban kwamitin yakin neman zabe na kasa na PDP, wanda shine gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ne ya sanar da hakan yayin jawabin da ya yi wa manema labarai a ranar Alhamis a Akure.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel