Kotu ta yanke hukuncin kisa a kan Trump, Sarki Salman da Yariman Saudiyya

Kotu ta yanke hukuncin kisa a kan Trump, Sarki Salman da Yariman Saudiyya

- Wata kotu a kasar Yemen ta yanke wa wasu mutane hukuncin kisa bisa harin saman da aka kai a Majz da ya kashe kananan yara a cikin mota kirar bas

- Cikin wadanda aka yanke wa hukuncin akwai Shugaba Donald Trump, Sarkin Saudiyya, Salman Bin Abdulaziz Al-Saud, da Yarima Mohammed Bin Salman Bin Abdulaziz Al-Saud

- Har wa yau kotun ta kuma yanke hukuncin cewa a biya iyalan yaran da aka kashe a harin saman na shekarar 2019 tarar Dalan Amurka Biliyan 10

Wata kotu a kasar Yemen ta zartar da hukuncin kisa a kan wasu mutum 10 ciki har da Shugaba Donald Trump, Sarki Salman Bin Abdulaziz Al-Saud, da Yarima Mohammed Bin Salman Bin Abdulaziz Al-Saud saboda aikata laifukan yaki.

Wata kotu ta zartar da hukuncin kisa a kan Trump, Sarki Salman da Yariman Saudiyya
Donald Trump da Salman Bin Abdulaziz Al-Saud
Asali: Twitter

An zartar da hukuncin ne a wani Kotu na musamman na masu manyan laifuka a Saada akan harin hadin gwiwa da aka kai wa wata motar bas cike da kananan yara a mazabar Majz.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa 'yan daba suka tube wa Fayose hula a Ondo

Amma wadanda aka yanke wa hukuncin ba su hallarci zaman shari'ar ba a kotun na 'yan Houthi kamar yadda Linda Ikeji Blog ya ruwaito.

Kafar watsa labarai mallakar Houthi a Yemen, SABA, ta tabbatar da yanke hukuncin kisar da aka yi wa Donald Trump, Salman Bin Abdulaziz Al-Saud, Mohammed Bin Salman Bin Abdulaziz Al-Saud, da Norton Schwartz saboda hannunsu a kai harin.

Sauran wadanda aka yanke wa hukuncin sun hada da Kwamandan Sojin Saman Saudiyya, Turki bin Bandar bin Abdulaziz, Shugaban kasar Yemen Abedrabbo Mansour Hadi, mataimakin shugaban kasar Yemen Ali Mohsen Saleh Al-Ahmar.

KU KARANTA: Masu garkuwa sun sace amaryar mai gidan burodi a Katsina

Farai minista Ahmed bin Dagher, Ministan Tsaro Muhammad Al-Maqdishi, da former tsohon sakataren tsaro na Amurka James Norman Mattis suma duk an yanke musu hukuncin kisar.

Kafar watsa labaran ta kuma ruwaito cewa kotun ta bukaci wadanda aka yi kararsu su biya iyalan yaran da aka kashe a harin saman na shekarar 2019 tarar Dalan Amurka Biliyan 10.

Har wa yau, kafar watsa labaran ta ce wadanda aka yanke wa hukuncin suna da damar daukaka kara.

A wani rahoton daban, Hukumar Tsaro ta NSCDC reshen Jihar Borno ta kama mutane hudu da ake zargin 'yan sakon 'yan kungiyar Boko Haram ne da jarkoki 34 na man fetur.

Daily Trust ta ruwaito cewa kwamandan hukumar na jihar, Ibrahim Abdullahi ne ya sanar da hakan yayin da ya ke gabatar da wadanda ake zargin a ranar Juma'a a Maiduguri.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164