Hotuna: Munir Jaafaru ya kai wa sabon Sarki ziyara, ya yi mubaya'a

Hotuna: Munir Jaafaru ya kai wa sabon Sarki ziyara, ya yi mubaya'a

- Daya daga cikin manema sarautar Zazzau, Munir Ja'afaru, ya kai wa sabon Sarkin Zazzau ziyara fadarsa dake Zaria

- Munir Ja'afaru yace yayi farin cikin nadin sarkin kuma yana tare da shi dari bisa dari domin su taru su ciyar da Zazzau gaba

- Dama yayi wa sabon Sarkin fatan alheri kuma ya taya shi da addu'ar samun damar sauke nauyin da Allah ya dora masa

Daya daga cikin manema sarautar Zazzau, Munir Ja'afaru ya ziyarci sabon Sarki, Ahmed Nuhu Bamalli, a fadarsa da ke cikin Zaria, jihar Kaduna.

Idan ba'a manta ba, a ranar Laraba, Gwamna Nasir El-Rufai ya nada Nuhu Bamalli a matsayin sarkin Zazzau, bayan rasuwar Sarki Shehu Idris a ranar Lahadi, 20 ga watan Satumba, bayan mulkar Zazzau na tsawon shekaru 45.

Munir Ja'afaru, Yariman Zazzau, ya sanar da manema labarai cewa zai dage wurin yin aiki tukuru tare da sabon Sarkin don samun cigaban masarautar Zazzau.

Dama kuma Yariman ya turo sakon taya murnarsa ga sabon Sarkin Zazzau, wanda Gwamna Nasir El-Rufai ya nada ranar Laraba.

A takardar da Ja'afaru ya tura, ya nuna amincewarsa da sabon Sarkin dari bisa dari, kuma yace haka Allah yaso.

Ya nuna matukar murnarsa, har yana yi wa sabon Sarkin addu'o'in samun lafiya, karfi da kuma ikon tafiyar da mulkinsa, da kuma sauke nauyin da Allah ya dora masa.

Hotuna: Munir Jaafaru ya kai wa sabon Sarki ziyara, ya yi mubaya'a
Hotuna: Munir Jaafaru ya kai wa sabon Sarki ziyara, ya yi mubaya'a. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: UGC

KU KARANTA: NASS ta hana wasu hadimai da ministocin Buhari rakiyar gabatar da kasafin kudi

Hotuna: Munir Jaafaru ya kai wa sabon Sarki ziyara, ya yi mubaya'a
Hotuna: Munir Jaafaru ya kai wa sabon Sarki ziyara, ya yi mubaya'a. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: UGC

KU KARANTA: Najeriya tana da miliyoyin jama'a da ke fama da tsananin talauci - Osinbajo

Hotuna: Munir Jaafaru ya kai wa sabon Sarki ziyara, ya yi mubaya'a
Hotuna: Munir Jaafaru ya kai wa sabon Sarki ziyara, ya yi mubaya'a. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: UGC

A wani labari na daban, daya daga cikin 'yan majalisar Sarkin Zazzau, Aminu Yakubu-Wambai, ya yi murabus daga sarautarsa ta Wakilin Raya Kasar Zazzau, bayan sa'o'i kadan da nada sabon sarkin Zazzau.

Idan za mu tuna, a ranar Laraba Gwamna Nasir El-Rufai ya nada Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau bayan rasuwar Dakta Shehu Idris a ranar 20 ga watan Satumba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel