Jama'a sun saki baki wurin kallon akuyar da ke yawo da kafafu biyu

Jama'a sun saki baki wurin kallon akuyar da ke yawo da kafafu biyu

- Wata akuya tayi tafiyar kusan mita 10 da kafafunta 2 kamar yadda mutane ke yi a kauyen Telwera, Bihar a kasar India

- Akuyar bata dogara da komai ba, face dage kafafunta 2 na gaba sama tana tafiya jama'a na kallonta suna yi mata bidiyo

- Al'amarin ya sa mutane daga kasashe daban-daban na duniya na son zuwa kauyen don ganin yadda akuyar ke tafiyar

Wata akuya a kasar India ta shayar da 'yan Kauyen Telwer, Bihar, mamaki, bayan ta dage kafafunta na gaba sama, tayi tafiya da kafafunta 2 na baya na tsawon sawu 33.

Bidiyon akuyar mai tafiya da kafafunta 2 yayi ta yaduwa a kafafen sada zumuntar zamani, inda kowa yayi ta al'ajabi.

Yayin da akuyar ke tafiyar, mutane da dama sun tsaya suna kallon wannan abin al'ajabi.

Kamar yadda jaridar New York Post ta ruwaito, masu akuyar sun dade suna koya mata tafiya da kafafu 2 kafin ta fito fili tayi.

Kamar yadda bidiyon ya bayyana, akuyar tayi tafiya tamkar mutum na kusan mita 10 a gaban mutane ba tare da ta dogara da komai da sauran kafafun nata na gaba ba.

'Yan kauyen sun koya mata tafiyar na tsawon awanni kafin ta bayyana gaban jama'a.

Al'amarin mai cike da ban al'ajabi yasa mutane daga kasashe da dama sha'awar zuwa kauyen da akuyar take, don ganin akuya mai tafiya da kafafunta 2.

KU KARANTA: Ahmed Lawan ya shawarci Buhari da ya guji cin bashi don aiwatar da manyan ayyuka

Jama'a sun saki baki wurin kallon akuyar da ke yawo da kafafu biyu
Jama'a sun saki baki wurin kallon akuyar da ke yawo da kafafu biyu. Hoto daga New York Post
Asali: UGC

KU KARANTA: Akwai yuwuwar maza masu babbar murya su fi sauran maza iya cin amana - Sabon bincike

A wani labari na daban, wata hira tsakanin saurayi da budurwa a kafar sada zumuntar zamani ta WhatsApp tayi ta yawo a yanar gizo. Saurayin, mai suna Stephen da budurwarsa sunyi hira ne akan shirin auren yayarta.

Bayan yayi ta tambayar budurwar ko za ta aureshi na tsawon shekaru 2 amma ta murje ido ta ki. Saurayin bayan ya ga cewa kullum tsufa yake yi, ya nuna lallai ya kosa yayi aure, sai ya sauya akalarsa zuwa yayarta.

A yadda saurayin yace, tunda budurwarsa mai shekaru 24 bata shirya ba, ya tabbatar yayarta mai shekaru 29 a shirye take tayi aure.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel