An yi zaman majalisar Sarki na farko karkashin Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli (Hotuna)
- Yan majalisar sarkia Zazzau sun halarci taron farko karkashin sabon sarki
- Sauran ya gidajen sarauta sun yi mubaya'a ga Sarki ahmed Nuhu Bamalli
- Mutum daya cikin yan majalisar sarki, Wakilin Raya Kasar Zazzau, ya yi murabus
Hakimai da iyalan tsohon Sarkin Zazzau, sun yi mubaya'a ga sabon Sarki, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli.
Mubaya'ar hakiman da iyalan tsohon Sarkin, ta biyo bayan naɗa Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau na 19 daga zuriyar Mallawa.
Wakilin Legit.ng Hausa da ya ziyarci fadar Zazzau a ranar Alhamis, ya ruwaito cewar, gwamnati ta tsaurara matakan tsaro a ciki da wajen fadar Sarkin.
Bayan karɓar gaisuwa daga hakiman, Alhaji Ahmad Bamalli, ya gana da ƴan majalisar Sarki, inda ya yi kira ga sauran masu neman Sarki, da su haɗa karfi da ƙarfe don samar da ci gaba a masarautar Zazzau da jihar Kaduna ba ki daya.
Kalli hotunan da muka kawo muku:

Asali: Original
KARANTA NAN: Sarkin Zazzau Ahmed Bamalli ya bukaci hadin-kai bayan ya hau gadon sarauta

Asali: Original

Asali: Original

Asali: Original
DUBA NAN: Gidajen Katsina da Barebari sun kai wa sabon Sarkin Zazzau gaisuwar ban-girma

Asali: Original
Mun kawo muku rahoton cewa daya daga cikin 'yan majalisar Sarkin Zazzau, Aminu Yakubu-Wambai, ya yi murabus daga sarautarsa ta Wakilin Raya Kasar Zazzau, bayan sa'o'i kadan da nada sabon sarkin Zazzau.
A wasikar murabus da Legit.ng ta gani, Wambai ya ce ya yi murabus ne saboda kan shi.
Kamar yadda wasikar ta bayyana, "Ina mika godiyata ga Allah da ya bani damar hawa wannan matsayin na Wakilin Raya Kasar Zazzau na 7, kuma dan majalisar masarautar Zazzau mai wakiltar karamar hukumar Kaduna ta Kudu."
"Ina son tabbatar wa da jama'a cewa murabus dina bashi da alaka da komai da suka wuce hidindimun kaina."
"Na yanke shawarar barin al'amuran fada domin samun damar mayar da hankali a kan ayyukana."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng