An cafke masu yi wa Boko Haram jigilar man fetur a Borno

An cafke masu yi wa Boko Haram jigilar man fetur a Borno

- Jami'an hukumar tsaro na NSCDC sunyi nasarar cafke wasu mutum hudu da ake zargin 'yan sakon 'yan ta'adda ne

- An kama mutanen hudu Usman Baptel, Alphonsus John, Nicholas Benjamin da Isaac Clement bisa zargin samarwa 'yan ta'addan man fetur

- An kama su ne dauke da jarkokin man fetur 34 shake da man fetur da suka boye cikin buhunna a kan babura

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa 'yan daba suka tube wa Fayose hula a Ondo

An cafke 'yan aiken 'yan Boko Haram su hudu dauke da jarkokin man fetur 34
An cafke 'yan aiken 'yan Boko Haram su hudu dauke da jarkokin man fetur 34. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Hukumar Tsaro ta NSCDC reshen Jihar Borno ta kama mutane hudu da ake zargin 'yan sakon 'yan kungiyar Boko Haram ne da jarkoki 34 na man fetur.

Daily Trust ta ruwaito cewa kwamandan hukumar na jihar, Ibrahim Abdullahi ne ya sanar da hakan yayin da ya ke gabatar da wadanda ake zargin a ranar Juma'a a Maiduguri.

Abdullahi ya ce daya daga cikin wadanda ake zargin, Usman Baptel shine manajan wani gidan mai a kauyen Husara da ke karamar hukumar Askira/Uba a jihar Borno.

KU KARANTA: Masu garkuwa sun sace amaryar mai gidan burodi a Katsina

Ya ce sauran sun hada da Alphonsus John, Nicholas Benjamin da Isaac Clement da aka kama a ranar 12 ga watan Satumba a kauyen Wastilla da ke karamar hukumar Michika da ke jihar Adamawa da ke makwabtaka da Borno.

Ya ce kayan da aka kama su da shi sun hada da jarkokin man fetur masu lauyin ruwan dorawa dauke da fetur kimanin lita 880 da aka boye su cikin buhunna a kan babura uku.

Abdullahi ya kuma bayyana cewa rundunar ta kama wadanda ake zargi da laifi 1,318 a wannan shekarar. An gama bincike kan 734 yayin da saura 468 ana kan bincikarsu kamar yadda kamfanin dillancin labarai NAN ta ruwaito.

A wani labarin, Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno a ranar Talata ya lissafa wasu hanyoyi da ya yi imanin idan sojoji sun bi za su iya cin galaba kan Boko Haram.

Gwamnan ya yi wannan jawabin ne wurin taron hadin gwiwa na shugaban sojojin ƙasa na shekarar 2020 da aka yi a Maiduguri a jihar Borno inda shine babban baƙo na musamman.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel