Shugaba Buhari ya mika godiya ga yan Najeriya bisa hakurin da sukeyi da shi

Shugaba Buhari ya mika godiya ga yan Najeriya bisa hakurin da sukeyi da shi

- Shugaban kasa ya bayyana gaban yan majalisar dokokin tarayya domin gabatar da kasafin kudin 2021

- Buhari ya jaddada niyyar gwamnatinsa na inganta rayuwan yan Najeriya gaba daya

- Ya godewa shugabannin majalisan dokokin tarayya bisa hadin kan da suke bashi da gwamnatinsa

Shugaba Muhammadu ya fara jawabinsa na gabatar da kasafin kudin 2021 da mika godiya ga yan Najeriya bisa hakuri, jajircewa da goyon bayan da suka cigaba da nunawa gwamnatinsa duk da halin kuncin da ake ciki.

Buhari ya bayyana cewa gwamnatin ta samu nasarori daban-daban a kasafin kudin 2020.

Shugaban kasan ya tunawa yan majalisan cewa an yi wasu sauye-sauye cikin kasafin kudin 2020 sakamakon bullar cutar Korona domin takaita illar da za ta yiwa tattalin arzikin kasar.

Ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta cigaba da kokarinta wajen samar da rana gobe mai kyau ga Najeriya.

Yace: "Mun godewa dukkan yan Najeriya bisa hakurinsu da cigaba da nuna mana goyon baya cikin wannan lokaci mai wuya."

"Zamu cigaba da kokarin cika manufarmu da samawa Najeriya rana gobe mai kyau."

KU KARANTA: Shugaba Buhari na gabatar da kasafin kudin 2021

Shugaba Buhari ya mika godiya ga yan Najeriya bisa hakurin da sukeyi da shi
Hoto: @Bashirahmaad
Asali: Twitter

Mun kawo muku cewa shugaba Buhari ya dira zauren majalisan misalin karfe 11 na safiyar Alhamis, 8 ga Oktoba, 2020.

Buhari ya yiwa sabon Kasafi mai kasafin kudin farfado da tattalin arziki da hakuri)

Yace: "Mun yi kiyasin wannan kasafin kudin bisa wadannan abubuwa:

1. Farashin danyen mai a $40 ga ganga

2. Zamu fitar da gangar mai 1.86 milyan kulli yaumin

3. Kudin canji N379 ga $1

4. GDP 3%, hauhawa kuma 11.95%

KARANTA: Masu zanga-zanga sun yi wa hedkwatar 'yan sanda zobe a Abuja

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel