KAI TSAYE: Shugaba Buhari na gabatar da kasafin kudin 2021
Komai ya kankama domin gabatar da kasafin kudin 2021 a gaban yan majalisar wakilai da na dattawa a hade.
Buhari ya shiga zauren majalisar misalin karfe 11:07 na safe kuma aka mike tsaye domin taken Najeriya.
Sannan shugaban majalisar dattawa ya yiwa shugaba Buhari maraba kuma ya umurci Sanata Tolu Olubiyi yayi addu'an Kiristoci kuma dan majalisa Maliki yayi na Musulmai.

Asali: Twitter

Asali: Twitter

Asali: Facebook

Asali: Twitter
Buhari ya gama jawabinsa, ya ajiye daftarin kasafin kudin kuma ya fita daga zauren majalisa
Shugaba Muhammadu Buhari ya fita daga majalisa bayan kammala gabatar da kasafin kudin 2021 .
Jawabin Buhari....
"Zamu karbo sabon bashin 4.82tr a shekarar 2021, " Buhari
Buhari ya yiwa sabon Kasafi mai kasafin kudin farfado da tattalin arziki da hakuri)
Mun yi kiyasin wannan kasafin kudin bisa wadannan abubuwa:
1. Farashin danyen mai a $40 ga gangan
2. Zamu fitar da gangar mai 1.86 milyan kulli yaumin
3. Kudin canji N379 ga $1
4. GDP 3%, hauhawa kuma 11.95%
Cewar Buhari
Jawabin Buhari
"Za mu kammala ginin gadar saman 2nd Niger kafin karewar wa'adinmu. Za mu kaddamar da Titin Legas zuwa Ibadan nan ba da dadewa ba." Buhari
"Zamu yaki yan bindiga, masu garkuwa da mutane da yan tada kura, " Buhari
Shugaba Buhari ya fara gabatar da jawabinsa ga yan majalisa
Ya jaddada niyyar tsamo yan Najeriya milyan 100 daga talauci cikin shekaru 10 masu zuwa. Ya ce gwamnatinsa zata dauki matasa 774,000 na ba da dadewa ba.
Shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, yana gabatar da jawabinsa
Ya yi magana kan illan da cutar Korona ta yiwa tattalin arzikin Najeriya da kuma irin hadin kai da kyakyyawan fahimtan dake tsakanin su da fadar shugaban kasa.