Allah ya yi wa shugaban NULGE, Ibrahim Khalil rasuwa

Allah ya yi wa shugaban NULGE, Ibrahim Khalil rasuwa

- Shugaban Kungiyar NULGE, Ibragim Khalil ya riga mu gidan gaskiya

- Marigayin wadda kuma shine ma'aji a kungiyar NLC ya rasu ne a ranar Laraba a Abuja

- Za a gudanar da jana'izar Ibrahim Khalil a karamar hukumar Wudil da ke jihar Kano

Allah ya yi wa shugaban NULGE, Ibrahim Khalil rasuwa
Allah ya yi wa shugaban NULGE, Ibrahim Khalil rasuwa. Hoto: @Lindaikeji
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ya ce Akeredolu ya cancanta ya yi tazarce a Ondo

Shugaban Kungiyar Ma'aikatan Kananan Hukumomi ta Kasa, (NULGE), Ibrahim Khaleel ya rasu kamar yadda Linda Ikeji Blog ta ruwaito.

A cewar wata majiya daga iyalansa, Khalil wanda kuma shine ma'ajin kungiyar kwadago ta kasa, NLC, ya yanke jiki ya fadi a ranar Laraba 7 ga watan Okotoba inda aka garzaya da shi asibiti a can aka tabbatar ya mutu.

DUBA WANNAN: Yadda rundunar sojojin Najeriya za ta yi nasarar yaƙi da Boko Haram - Zulum

Shugaban kungiyar NULGE reshen jihar Kano, Abdullahi Muhammadu Gwarzo ya tabbatar wa manema labarai rasuwar Khalil.

Ya ce za a yi wa marigayin jana'iza a karamar hukumar Wudil a ranar Alhamis 8 ga watan Oktoban shekarar 2020.

A wani labarin daban, Shugaba Buhari ya nuna bakin cikinsa bisa rasuwar Farfesa Abdulahamin Dutse, tsohon shugaban Asibitin Koyarwa Ta Aminu Kano, inda ya ce mutuwarsa "babban rashi ne ga bangaren likitanci."

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne cikin sakon ta'aziyya da ta fito daga bakin kakakinsa Garba Shehu a ranar Laraba a Abuja.

A cewarsa, rasuwar Farfesa Dutse ya tauye wa Najeriya daya daga cikin manyan likitocin da suka sadaukar da kansu wurin aikinsu.

Ya kara da cewa an rasa marigayin ne a lokacin da kasar ke bukatarsa sosai sannan ya ce za ayi kewarsa.

Shugaban kasar ya yi addu'ar Allah ya jikan marigayin ya saka masa da gidan aljanna ya bawa wadanda ya bari hakurin jure rashinsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel