Da duminsa: Masu zanga-zanga sun yi wa hedkwatar 'yan sanda zobe a Abuja

Da duminsa: Masu zanga-zanga sun yi wa hedkwatar 'yan sanda zobe a Abuja

- Daruruwan masu zanga-zangar lumana sun zagaye hedkwatar 'yan sandan Najeriya a Abuja

- Suna dauke da fastoci inda suke bukatar a kawo karshen rashin adalcin da 'yan sandan ke yi

- Suna zuba jan fenti a kan babban titin Shehu Shagari da ke Abuja domin alamun nuna zubar jini

Masu zanga-zanga da ke bukatar a gyara tsarin 'yan sanda na musamman da ke yaki da fashi da makami a fadin kasar nan sun zagaye hedkwatar 'yan sandan Najeriya da ke Abuja.

Masu zanga-zangar suna kan babbar hanyar Shehu Shagari inda suke ta ihun a kawo karshen SARS yayin da suka takaita kaiwa da kawowar ababen hawa.

A wannan halin, suna rike da takardu masu rubuce-rubuce daban-daban duk suna nuna bukatarsu, The Punch ta wallafa.

Masu zanga-zangar sun dinga watsa jan fenti a kan tituna domin nuna yadda jami'an SARS ke zubda jinii tare da kashe-kashe.

Suna zargin jami'an 'yan sandan na musamman da iya take hakkin dan Adam da ya hada da kisa, karbar kudi, tsare jama'a ba tare da shari'a ba da sauransu.

KU KARANTA: Matar aure ta wallafa sunan mijinta a kafar sada zumunta a kan karya da yayi mata ya tare da karuwa a otal

Da duminsa: Masu zanga-zanga sun yi wa hedkwatar 'yan sanda zobe a Abuja
Da duminsa: Masu zanga-zanga sun yi wa hedkwatar 'yan sanda zobe a Abuja. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: A karon farko, tsohuwar matar Fani Kayode ta magantu a kan mutuwar aurensu

A wani labari na daban, Sifeta janar na 'yan sanda, M.A Adamu ya dakatar da ma'aikatan FSARS daga cigaba da ayyukansu, sakamakon korafin da 'yan Najeriya suke yi akan 'yan sanda na ta'addanci.

Ba su kadai wannan umarnin ya shafa ba, har da ma'aikatan STS, IRT da kuma ACS. An dakatar da ma'aikatan daga yin ayyuka kamar sintiri, tsayawa bincike, ba da hannu da sauran ayyukan da suke yi a kan tituna.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel