Kotu ta raba auren shekara 7 a kan rashin biyan kudin makaranta

Kotu ta raba auren shekara 7 a kan rashin biyan kudin makaranta

- Wata kotu dake zama a Kubwa, Abuja ta tsinke igiyar auren shekara 7 dake tsakanin Salamat da Isiyaka

- Kamar yadda Salamat ta gabatar wa alkali kara, tace Isiyaka baya sauke nauyinsa a matsayin mijinta kuma uban 'ya'yanta

- Tace baya biya wa yaransu kudin makaranta da sauran bukatunsu na yau da kullum, ita kadai take yin komai

Wata kotu dake zama a Kubwa, Abuja ta tsinke igiyar aure mai shekaru 7, ranara Laraba, tsakanin Salamat Dauda da mijinta, Isiyaka, akan kin biya wa yaransa kudin makaranta.

Salamat ta roki kotu da ta tsinke igiyar aurenta da Isiyaka saboda rashin sauke nauyinsa a matsayin mijinta kuma uban 'ya'yanta.

Alkali mai shari'a, Muhammad Adamu, ya ce matar za ta yi zaman iddah na watanni 3 kafin ta sake wani auren.

Salamat ta shaida wa kotu yadda Isiyaka ya ki sauke nauyinsa a matsayin mijinta kuma mahaifi ga yaranta.

Ta ce, "Ni da kaina nake biya wa yaranmu kudin makaranta da sauran bukatun gida. Na gaji da halayensa, ni nake yin komai."

A don haka ne ta roki kotu ta kwance igiyar aurensu da aka yi bisa shari'ar Musulunci a ranar 28 ga watan Afirilu, 2013.

Isiyaka dake aiki a wani kamfanin gine-gine a Abuja ya amince da rabuwa da matar tasa, a cewarsa, yayi iyakar kokarinsa.

KU KARANTA: A karon farko, tsohuwar matar Fani Kayode ta magantu a kan mutuwar aurensu

Kotu ta raba auren shekara 7 a kan rashin biyan kudin makaranta
Kotu ta raba auren shekara 7 a kan rashin biyan kudin makaranta. Hoto daga Daily Trust
Asali: Facebook

KU KARANTA: Saurayi zai yi wuff da yayar budurwarsa bayan budurwar ta ki aurensa

A wani labari na daban, wata mata ta tura wa wata mai kula da wata kungiyar ta kafar sada zumuntar zamani ta Facebook sako, wanda ta fallasa mata mijin ta mai suna Felix Ogiri.

Ta ce Felix na hawa wata mota kirar Range Rover. A cewar ta, yayi ikirarin zai yi tafiya zuwa jihar Delta, amma tana ganinsa cikin gari, kuma tasan Otal din da ya sauka tare da wata mata. Ta kara da cewa, yaransu na gida saboda yaki biya musu kudin makaranta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel