Da duminsa: Daya daga cikin 'yan majalisar masarautar Zazzau ya yi murabus

Da duminsa: Daya daga cikin 'yan majalisar masarautar Zazzau ya yi murabus

- Aminu Yakubu Wambai, daya daga cikin 'yan majalisar masarautar Zazzau ya yi murabus

- Hakan ya faru bayan sa'o'i kadan da Gwamna El-Rufai ya nada Ambasada Bamalli a sabon Sarki

- Amma kuma Wambai ya ce murabus din sa bashi da wata alaka da halin da ake ciki

Daya daga cikin 'yan majalisar Sarkin Zazzau, Aminu Yakubu-Wambai, ya yi murabus daga sarautarsa ta Wakilin Raya Kasar Zazzau, bayan sa'o'i kadan da nada sabon sarkin Zazzau.

Idan za mu tuna, a ranar Laraba Gwamna Nasir El-Rufai ya nada Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau bayan rasuwar Dakta Shehu Idris a ranar 20 ga watan Satumba.

Da duminsa: Daya daga 'yan majalisar masarautar Zazzau ya yi murabus
Da duminsa: Daya daga 'yan majalisar masarautar Zazzau ya yi murabus. Hoto daga Abdulaziz Umar Gwarzo
Asali: Facebook

Daily Nigerian ta ruwaito cewa Wambai dan majalisar masarautar Zazzau ne mai wakiltar Kaduna ta kudu. Ya rike wannan sarautar na tsawon shekaru 19.

A wasikar murabus da Legit.ng ta gani, Wambai ya ce ya yi murabus ne saboda kan shi.

Kamar yadda wasikar ta bayyana, "Ina mika godiyata ga Allah da ya bani damar hawa wannan matsayin na Wakilin Raya Kasar Zazzau na 7, kuma dan majalisar masarautar Zazzau mai wakiltar karamar hukumar Kaduna ta Kudu.

"Ina son tabbatar wa da jama'a cewa murabus dina bashi da alaka da komai da suka wuce hidindimun kaina. Na yanke shawarar barin al'amuran fada domin samun damar mayar da hankali a kan ayyukana."

KU KARANTA: NASS ta hana wasu hadimai da ministocin Buhari rakiyar gabatar da kasafin kudi

KU KARANTA: Najeriya tana da miliyoyin jama'a da ke fama da tsananin talauci - Osinbajo

A wani labari na daban, labari da duminsa da ke zuwa wa Legit.ng shine sanarwar gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai na sabon Sarkin Zazzau.

Kamar yadda Gwamnan jihar Kaduna ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya bayyana Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau na 19.

Ya gaji marigayi mai martaba, Alhaji Dakta Shehu Idris wanda ya rasu a ranar Lahadi, 20 ga watan Satumban 2020 bayan kwashe shekaru 45 da yayi a karagar mulkin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel