Makarfi ya yi martani a kan nadin Sarki Ahmed Bamalli Zazzau

Makarfi ya yi martani a kan nadin Sarki Ahmed Bamalli Zazzau

- Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Sanata Ahmed Muhammed Makarfi, ya tura sakon taya murnarsa ga sabon Sarkin Zazzau

- Sanata Makarfi ya bayyana farin cikinsa da tabbatar da amincewarsa dari bisa dari akan nadin sabon sarkin

- Ya kuma yi masa addu'ar samun lafiya, kwarin guiwa, jajircewa da dagewa wurin sauke wannan nauyi da Allah ya dora masa

Tun bayan nadin sabon sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli, mutane da dama ke ta fitowa suna taya shi murna da bashi kwarin guiwa.

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Sanata Ahmed Muhammed Makarfi ba'a barshi a baya ba.

Ya fito a fili ya nuna wa duniya yadda yayi na'am da nadin Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau na 19, kuma shugaban majalisar sarakunan jihar Kaduna.

Makarfi ya turo wasikar taya murnarsa ga sabon Sarkin a ranar Laraba, 7 ga watan Oktoba 2020.

Ga abinda wasikar tasa ta kunsa: "Na yarda da cewa, sabon Sarkin da aka nada zai yi amfani da fasaharsa wurin tafiyar da mulkin Zazzau cikin inganci, duk da kasancewar majalisar sarakunan jihar Kaduna cike take da kalubale iri-iri.

"Ina da tabbacin sabon Sarkin da aka nada, zai zama tamkar bango ne ga jama'ar Zazzau da kewaye.

"Ina masa fatan alkhairi da addu'ar samun karfi, lafiya, jajircewa da kuma juriya wurin sauke wannan nauyi da Allah ya dora masa. Allah ya ci gaba da kare shi da yi masa jagora."

KU KARANTA: Auren Hausawa: Dukkan abinda ya kamata a sani daga nema zuwa samun auren

Makarfi ya yi martani a kan nadin Sarki Ahmed Bamalli Zazzau
Makarfi ya yi martani a kan nadin Sarki Ahmed Bamalli Zazzau. Hoto daga @Dailytrust
Asali: Twitter

KU KARANTA: An rasa rai 1 bayan rumfar kasuwa ta rushe a kasuwar Kurmi da ke Kano

A wani labarai na daban, labari da duminsa da ke zuwa wa Legit.ng shine sanarwar gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai na sabon Sarkin Zazzau.

Kamar yadda Gwamnan jihar Kaduna ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya bayyana Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau na 19.

Ya gaji marigayi mai martaba, Alhaji Dakta Shehu Idris wanda ya rasu a ranar Lahadi, 20 ga watan Satumban 2020 bayan kwashe shekaru 45 da yayi a karagar mulkin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel