Dalilin da yasa 'yan daba suka tube wa Fayose hula a Ondo

Dalilin da yasa 'yan daba suka tube wa Fayose hula a Ondo

- Wasu matasa da ake kyautata zaton 'yan daban siyasa ne masu goyon bayan Gwamna Makinde sun ci mutuncin Ayo Fayose a Ondo

- Matasan sun taso wa tsohon gwamnan Ekiti sannan daya daga cikinsu ya saka hannu ya fizge hular da ke kan Fayose

- Wasu majiyoyi sun ce rikicin siyasa ta jagorancin jam'iyyar a PDP na yankin Kudu maso Yamma da ke tsakanin Fayose da Makinde ne ta janyo aka masa wannan cin mutuncin

Hular tsohon gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose ta bace a birnin Ondo a wurin taron rufe yakin neman zaben jam'iyyar PDP gabanin zaben gwamna da za ayi a jihar a ranar Asabar 10 ga watan Oktoba.

A lokacin da Fayose yake kan hayarsa zuwa mimbari a wurin taron, 'yan daba sun nufi inda ya ke kuma daya daga cikinsu ya fizge hular da ke kansa mai dauke da rubutun 'Eyitayo'.

DUBA WANNAN: Yadda rundunar sojojin Najeriya za ta yi nasarar yaƙi da Boko Haram - Zulum

Dalilin da yasa 'yan taba suka tube wa Fayose hula a Ondo
Dalilin da yasa 'yan taba suka tube wa Fayose hula a Ondo. Hoto: PM News
Asali: Twitter

Jim kadan bayan hakan, 'yan daban sun bawa hammata iska tsakaninsu da masu tsaron Fayose.

Pulse ta ruwaito cewa rikicin siyasa da ake yi a yankin ne ya janyo hakan.

Majiyoyi sun ce an kunyata Fayose ne saboda rikicin da ke tsakaninsa da Gwamnan Oyo Seyi Makinde.

"Fayose ya rika sukar Makinde kan rikicin PDP a Ekiti. Fayose ya jagoranci wasu masu ruwa da tsaki a jam'iyyar PDP zuwa wurin shugaban jam'iyyar Uche Secondus don kokawa kan irin babakeren da Makinde ke yi. Fayose na son zama jagoran jam'iyyar PDP a Kudu maso Yamma da Ekiti amma Makinde bai yarda da hakan ba.

KU KARANTA: Hatsarin mota ta yi sanadin rasa rayyuka 9 a Kano

"Sanata Abiodun Olujimi da Fayose sun dade suna sa-in-sa kan wanda zai zama jagoran PDP a Ekiti.

"Olujumi na ganin ita ce ya kamata ta zama jagora tunda itace Sanata tilo na PDP da ke wakiltan yankin. Makinde yana goyon bayan ta domin yana ganin Fayose ya cika son girma.

"Cin mutuncin da yaran suka yi wa Fayose sako ne. Yaran sun tube hular Fayose a fili don yin mubaya'a ga Makinde," a cewar wata majiya kusa da PDP.

A martaninsa, Fayose ya dora laifin cin mutuncin da aka yi masa kan Makinde da mataimakin PDP na kasa, Cif Bode Goerge.

Ya bayyana hakan ne ta bakin kakakinsa Lere Olayinka inda yace hakan ba za ta hana shi cigaba da fadin gaskiya a yankin na kudu maso yamma ba.

Ya kwatanta abinda ya faru da shi da abinda ya faru da marigayi Bola Ige da shima aka taba cire masa hula a Ile Ife.

Shugaba Buhari ya bayyana goyon bayansa ga tazarcen da gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ke neman yi.

Gwamnan da aka zaɓa a karon farko a 2017 yana fatar zarce wa kan mulki idan al'ummar jihar sun dake zabensa a zaɓen da za ayi ranar Asabar 10 ga watan Oktoba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel