Shugabancin ƙasa: Za mu goyi bayan Igbo a 2023 - Sarkin Hausawa

Shugabancin ƙasa: Za mu goyi bayan Igbo a 2023 - Sarkin Hausawa

- Al'ummar hausawa mazauna jihar Cross Rivers sun ce a shirye suke su mara wa 'yan yankin kudu maso gabas baya don fitar da shugaban kasa a 2023

- Sarkin Hausawa na jihar Cross Rivers, Alhaji Salisu Lawan Abba ne ya yi wannan furucin yayin da mambobin kungiyar Ohanaeze Ndigbo suka kai masa ziyara a fadarsa

- Sarkin ya ce za su wayar da Hausawa da Fulani kan dalilan da yasa ya kamata a bawa 'yan Kudu maso gabas damar fitar da shugaban kasa idan har ana ikirarin cewa Najeriya ta kowa ne

Shugabancin ƙasa: Za mu goyi bayan Igbo a 2023 - Sarkin Hausawa
Shugabancin ƙasa: Za mu goyi bayan Igbo a 2023 - Sarkin Hausawa. Hoto: @nairaland
Asali: Twitter

Hausawa mazauna jihar Cross Rivers sun yi wa ƙungiyar Ohanaeze Ndigbo alƙawarin cewa za su mara wa yankin Kudu maso Gabas baya a yunkurin su na ganin shugaban Najeriya ya fito daga yankin a 2023.

Shugaban Hausawa da Fulani a jihar, Alhaji Salisu Abba Lawan ne ya bayyana hakan a yayin da mambobin Ohanaeze Ndigbo suka ziyarci fadarsa da ke Bogobiri a Calabar.

DUBA WANNAN: Yadda rundunar sojojin Najeriya za ta yi nasarar yaƙi da Boko Haram - Zulum

Lawan ya ce, "Ina son yi wa Ohanaeze Ndigbo godiya saboda ziyarar da suka kawo mana don ƙarfafa danƙon zumunci tsakanin Hausawa da Fulani da ƴan uwansu Igbo a jihar.

"Ba zamu cigaba da iƙirarin cewa dukkan mu ƴan kasa daya bane idan har mun ware wani ɓangare na ƙasar daga shugabanci. Ina baku tabbacin cewa zamu wayar da kan Hausawa da Fulani a jihar kan dalilan da yasa ya kamata a bawa Igbo damar fitar da shugaban kasa a 2023."

KU KARANTA: Hatsarin mota ta yi sanadin rasa rayyuka 9 a Kano

Tunda farko shugaban Ohanaeze Ndigbo na jihar, Ugorji Nwabueze da ya jogaranci tawagar ya ce neman ganin anyi adalci ne yasa Kudu maso Gabas ke neman ganin an basu damar fitar da shugaban ƙasa.

A wani labarin daban, Shugaba Buhari ya nuna bakin cikinsa bisa rasuwar Farfesa Abdulahamin Dutse, tsohon shugaban Asibitin Koyarwa Ta Aminu Kano, inda ya ce mutuwarsa "babban rashi ne ga bangaren likitanci.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne cikin sakon ta'aziyya da ta fito daga bakin kakakinsa Garba Shehu a ranar Laraba a Abuja.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel