Rayuka 5, gidaje 89, shaguna 47 sun salwanta a fashewar tankar Gas a Legas (Hotuna)

Rayuka 5, gidaje 89, shaguna 47 sun salwanta a fashewar tankar Gas a Legas (Hotuna)

- Akalla gawawwaki biyar aka samu a fashewar tankar Gas a Baruwa, Legas

- Daga cikin asarar da akayi akwai Coci da makarantar da suka kone

- An garzaya da mutane da gobarar ta shafa asibiti mafi kusa da Baruwa

Wani fashewa ya sake faruwa a tashar iskar Gas dake unguwar Baruwa na karamar hukumar Alimosho dake jihar Legas.

An tattaro cewa gobarar ta faru ne misalin karfe 05:45 na asuban ranar Alhamis.

Wakilin Legit.ng Tobi Bolashodun ya garzaya wajen domin kawo muku bayanai kai tsaye.

Legit ta tattaro cewa har yanzu ba'a san adadin wadanda suka rasa rayukansu ba amma mun tabbatar da wasu sun jigata kuma an garzaya da su asibiti.

Bayan rayuka biyar da suka salwanta, akalla mutane uku sun jikkata. Hakazalika gidaje, shaguna makaranta, coci da motoci sun kone.

Rahoton Thisday ya nuna cewa:

Shaguna 89 sun kone;

Gidaje 47 (Da coci, makaranta da gidan biki) sun kone;

Falwaya 23 sun kone;

Taransfoma biyu sun yi bindiga;

Tankokin iskar gas sun yi bindiga

Keke Napep da babur daya sun kone

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya mika godiya ga yan Najeriya bisa hakurin da sukeyi da shi

A cewar masu idanuwan shaida, wata tankar iskar gas ce ta fashe yayinda take juye iskan a tashar gas na Best Roof.

An tattaro cewa fashewar ta faru ne sakamakon injin Janareto dake kunne lokacin da ake juye iskar gas din.

Yayinda tankar ta fashe, dukka sauran tankokin gas dake kusa suka kama da wuta.

Jagoran hukumar bada agaji na gaggawa NEMA na yankin kudu maso yamma, Mr Ibrahim Farinloye, ya ce da wuri jami'an bada agaji suka garzaya wajen, Thisday ta ruwaito.

Ya ce an tsinci gawawwaki biyar yayinda aka garzaya wata mata da yara biyu asibiti saboda kuna.

Yanzu-yanzu: Wani fashewa ya sake aukuwa a jihar Legas yanzu haka
Yanzu-yanzu: Wani fashewa ya sake aukuwa a jihar Legas yanzu haka
Asali: UGC

DUBA NAN: Shugaba Buhari na gabatar da kasafin kudin 2021

Yanzu-yanzu: Wani fashewa ya sake aukuwa a jihar Legas yanzu haka
Yanzu-yanzu: Wani fashewa ya sake aukuwa a jihar Legas yanzu haka
Asali: UGC

Yanzu-yanzu: Wani fashewa ya sake aukuwa a jihar Legas yanzu haka
Yanzu-yanzu: Wani fashewa ya sake aukuwa a jihar Legas yanzu haka
Asali: UGC

Yanzu-yanzu: Wani fashewa ya sake aukuwa a jihar Legas yanzu haka
Yanzu-yanzu: Wani fashewa ya sake aukuwa a jihar Legas yanzu haka
Asali: UGC

Kwanaki 13 yau da wata tankar mai ta yi tashin Bam kuma ta kama da wuta ranar Alhamis a Cele Bus Stop, Iju Ishaga dake jihar Legas kuma mutane da dama sun jiggata.

Dirakta Janar na hukumar kai agaji na gaggawa na jihar Legas LASEMA, Dr. Olufemi Oke-Osanyintolu ya tabbatar da aukuwar hakan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel