Masu garkuwa sun sace amaryar mai gidan burodi a Katsina

Masu garkuwa sun sace amaryar mai gidan burodi a Katsina

- 'Yan bindiga sun kai hari kauyen Kafin Soli a Katsina sun sace matar mai gidan biredi

- Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina SP Gambo Isah ya tabbatar da afkuwar lamarin

- Ana zargin 'yan bindigan sun kai harin ne saboda bayanan sirri da mazauna kauyen ke bawa jami'an tsaro

Gungun 'ƴan bindiga sun mamaye ƙauyen Kafin Soli da ke ƙaramar hukumar Kankiya a jihar Katsina inda suka ɗauke matar sanannen mai gidan burodi a yankin, Ahmed Muhammad.

Muhammad shine mamallakin gidan burodin Safiya (Safiya Bread) a ƙauyen Kafin Soli.

Masu garkuwa sun sace amaryar mai gidan burodi a Katsina
Masu garkuwa sun sace amaryar mai gidan burodi a Katsina. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yadda rundunar sojojin Najeriya za ta yi nasarar yaƙi da Boko Haram - Zulum

Mazauna yankin sun shaidawa masu rahotanni cewa 'ƴan bindigar sun mamaye ƙauyen tun karfe 12 na dare inda suka shafe awa uku suna gudanar da ayyukan su kafin daga bisani su sace amaryar zuwa inda ba'a sani ba a kan babura.

Wani mazaunin ƙauyen ya shaidawa 'ƴan jarida cewa ana zargin 'ƴan bindigar sun zo ramuyar gayya ne sakamakon kama masu kai musu bayanai da jami'an tsaro suka yi.

"Sun kawo harin ramuyar gayya ne saboda basu ji daɗin yadda aka tona asirin masu basu bayanai a gun jami'an tsaro ba wanda hakan yayi sanadiyyar kama masu basu bayanan,"a cewarsa.

KU KARANTA: Hotuna: Ku sadu da sabon Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli

Ya kuma ƙara da cewa wata ƙila jami'an tsaro sun yi amfani da na'urar bin diddigi don gano masu basu bayanan a kusa da rugar da ke gab da ƙauyen.

Yace 'ƴan bindigar sun kawo hari aƙalla sau biyar kauyen sakamakon bayanan da suke samu daga masu basu bayanan.

Mai magana da yawun 'ƴan sanda jihar Katsina, SP Gambo Isah ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace hukumar 'ƴan sanda tana gudanar da bincike don tabbatar da sun gano masu laifin domin su gurfanar dasu a gaban kotu don su girbi abin da suka shuka

A wani labarin daban, Gwamnatin tarayya ta bada umurnin masu amfana da shirin N-Power na Batch A da B da ba su samu kudadensu na watanni baya ba su tafi ofisoshin wakilansu na jihohi domin sake tantance su.

Ministan jin kai da kare afkuwar balai, Sadiya Umar Faruk ce ta bada wannan umurnin a ranar Talata kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel