Dukkan masu rajin yakin neman Biyafara mahaukata ne - Babban Malamin Katolika

Dukkan masu rajin yakin neman Biyafara mahaukata ne - Babban Malamin Katolika

- Karon farko, wani babban daga kudancin Najeriya ya soki masu yakin neman Biyafara

- Rabaran Uma Ukpai ya ce sai Najeriya ta hada kanta za'a samu cigaba

- Ya yi kira ga yan Najeriya su so juna kuma su rika damuwa da juna

Shahararren malamin addinin Kirista, Rabaran Uma Ukpai, ya ce masu yakin neman Biyafara a yankin kudu maso gabashin Najeriya duk mahaukata ne.

Yayinda yake hira da manema labarai a hedkwatar cocinsa dake Uyo, faston ya caccaki kiraye-kirayen da kungiyoyin yakin neman yancin Biyafara irinsu MASSOB da IPOB keyi.

Ya ce duk wanda yake neman yan kabilar Igbo su balle daga Najeriya ya tabbatar da cewa yana da tabin hankali.

"Dama akwai mahaukata, ko da kuna ganin kaman suna da hankali. Duk wanda ke yakin neman Biyafara ya nuna nauyin haukarsa," yace.

Malamin wanda yayi tsokaci kan cikan Najeriya shekaru 60 da samun yanci daga hannun turawan mulkin mallaka ya ce har yanzu akwai masu kokarin raba kan kasar.

A cewarsa, Najeriya ba zata cigaba ba muddin ba'a son juna da ganin girman juna.

"A matsayinmu na kasa sai mun so juna zamu cigaba. Amma a Najeriya, babu ruwanmu ko makwabcinmu ya koshi kuma bamu ganin girman juna," Ya kara

KU KARANTA: Jerin abubuwa masu muhimmanci 20 da suka faru daga 1960 zuwa 2020

Dukkan masu rajin yakin neman Biyafara mahaukata ne - Babban Malamin Katolika
Credit: The Nation Newspaper
Asali: UGC

DUBA NAN: Jihohi 9 ne masu arziki a Najeriya, 12 matsiyata ne kuma duk Arewa suke - Masanin Tattalin arziki

A baya mun kawo muku rahoton cewa kungiyar yan kabilar Igbo a Najeriya, Ohanaeze Ndigbo, ta ce idan Najeriya ta samu shugaban kasa Igbo a shekarar 2023, za a ga sauyi a kasar.

Shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo, Nnia Nwodo, ya bayyana hakan ne a sakon murnar da ya aikawa dan Najeriya, Kelechi Madu, wanda aka nada Ministan Shari'a a kasar Canada.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel