Buhari ya sake nada Fidet Okhiria a matsayin shugaban NRC

Buhari ya sake nada Fidet Okhiria a matsayin shugaban NRC

- Shugaba Muhammadu Buhari ya sake nada Fidet Freeborn Okhiria a matsayin shugaban hukumar NRC

- Sanarwar sabunta nadin ta fito ne daga bakin sakatariyar dindidin na ma'aikatar sufuri, Magdalene Ajani

- karkashin jagorancinsa an kammala aikin layin dogo na Abuja-Kaduna da Itakpe-Warri kuma ana daf da kammala na Lagos-Ibadan

Buhari ya sake nada Fidet Okhiria a matsayin shugaban NRC
Buhari ya sake nada Fidet Okhiria a matsayin shugaban NRC. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

KARANTA NAN: Kishi ya saka ango ya kashe amaryarsa da duka a wurin bikin aurensu a Rasha

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sabunta wa'addin shugaban Hukumar Jiragen Kasa ta Najeriya, NRC, Fidet Okhiria na tsawon shekaru hudu.

Sakatariyar dindindin na Ma'aikatar Sufuri, Dakta Magdalene Ajani ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwar da ta raba wa manema labarai kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A wata wasika mai lamba No SH/COS/17/A/1698 mai dauke da kwanan wata 5 ga watan Oktoban 2020, ta ce nadin ya dace da sashi na dokar Hukumar Jiragen Kasa na Act. Cap 129, LFN, 2004.

DUBA WANNAN: Hatsarin mota ta yi sanadin rasa rayyuka 9 a Kano

An fara nada Injiniya Fidet Freeborn Okhiria ne matsayin shugaban na NRC a ranar 24 ga watan Oktoban 2016, kuma an sabunta nadinsa daga ranar 20 ga watan Oktoba a karo na biyu kuma na karshe.

A karkashin jagorancinsa an kammala aikin layin dogo na Abuja-Kaduna da Itakpe-Warri kuma ana daf da kammala na Lagos-Ibadan.

A wani labarin daban, Gwamnatin tarayya ta bada umurnin masu amfana da shirin N-Power na Batch A da B da ba su samu kudadensu na watanni baya ba su tafi ofisoshin wakilansu na jihohi domin sake tantance su.

Ministan jin kai da kare afkuwar balai, Sadiya Umar Faruk ce ta bada wannan umurnin a ranar Talata kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel