Kano: An damke wani da katunan ATM kimanin 5500 boye cikin buhun wake yana kokarin tafiya Dubai

Kano: An damke wani da katunan ATM kimanin 5500 boye cikin buhun wake yana kokarin tafiya Dubai

- Kasa da wata guda da damke wani, an sake damke matafiyi da katin ATM yana kokarin shillawa Dubai

- Yan Najeriya sun yi kaurin suna da damfarar mutane a kasar Larabawan

- Kwanakin baya an damke yan Najeriya, Hushpuppi, Woodberry da Mompha, duka masu damfara a Dubai

Jami'an hukumar Kwastam a Najeriya, shiyyar Kano/Jigawa sun damke wani matafiyin da ya nufi Dubai, UAE da katunan cire kudi watau ATM guda 5,342 a tashar jirgin saman Malam Aminu Kano dake jihar Kano.

Kwantrolan Kwastam na yankin, Nasir Ahmed, ya bayyana hakan ne yayinda yake mika mutumin ga hukumar hana almundahana EFCC, ranar Laraba a Kano, Daily Nigerian ta ruwaito.

Ahmed ya ce jami'ansa ne suka damke mutumin yayinda yake kokarin shiga cikin jirgin Ethiopian Air da ta nufi Dubai da katunan boye cikin buhuhunan wake biyu.

Kano: An damke wani da katunan ATM kimanin 5500 boye cikin buhun wake yana kokarin tafiya Dubai
Kano: An damke wani da katunan ATM kimanin 5500 boye cikin buhun wake yana kokarin tafiya Dubai
Asali: Twitter

A wani labarin daban, 'Yan bindiga sun kashe jami'in hukumar yaki da masu fasakwabri wato kwastam yayin da ya ke bakin aikinsa a kauyen Dan Arau da ke babban titin Katsina/Jibya.

Sun kashe Garba Nasiru, mai mukamin mataimakin sufritanda ne yayin wani hari mai ban mamaki da suka kai a ranar Juma'a sannan suka tafi da bindigarsa AK 47.

DUBA NAN: Jihohi 9 ne masu arziki a Najeriya, 12 matsiyata ne kuma duk Arewa suke - Masanin Tattalin arziki

The Punch ta ruwaito cewa sai da aka yi bata-kashi da jami'an tsaro sannan suka yi nasarar kwato gawarsa daga hannun 'yan bindigan inda suka tsere suka shiga cikin daji.

Rahotanni sun nuna cewa tuni an yi wa jami'in jana'iza bisa koyarwar addinin musulunci duk da cewa kokarin da aka yi na ji ta bakin kakakin rundunar na Katsina bai yi wu ba.

KARANTA WANNAN: Majalisar wakilai ta rincabe da hayaniya yayinda mambobi 2 suka sauya sheka daga PDP zuwa APC

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel