Shugaba Buhari ya ce Akeredolu ya cancanta ya yi tazarce a Ondo

Shugaba Buhari ya ce Akeredolu ya cancanta ya yi tazarce a Ondo

- Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya nuna goyon bayansa ga tazarcen Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo

- Shugaban kasar ya ce ya gamsu da irin kamun ludayin gwamnan kuma ya yi imanin zai bawa maraɗa kunya idan ya zarce

- Buhari ya yi kira da al'ummar jihar su zabi Gwamna Akeredolu don ya cigaba da ayyukan alheri da ya fara

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana goyon bayansa ga tazarcen da gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ke neman yi.

Gwamnan da aka zaɓa a karon farko a 2017 yana fatar zarce wa kan mulki idan al'ummar jihar sun dake zabensa a zaɓen da za ayi ranar Asabar 10 ga watan Oktoba.

DUBA WANNAN: Yadda rundunar sojojin Najeriya za ta yi nasarar yaƙi da Boko Haram - Zulum

Buhari, a ranar 7 ga watan Oktoba ya ce ya gamsu da irin kamun ludayin gwamnan kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Ya ce gwamnan mai shekaru 64 abinda alfahari ne ga jam'iyyar All Progressives Congress, APC inda ya ce ya gamsu da nasarorin da ya samu a wa'adin mulkinsa na farko duba da irin kuɗin ta ya tarar a jihar.

"Ya dace a bawa Gwamna Akeredolu dama ya zarce don cigaba da ayyuka masu kyau da ya fara a wa'adinsa na farko.

"Baya ga alfahari da nasarorinsa; Ina kyautata zaton mutanen jihar Ondo za su sake zaben shi karo biyu," in ji shugaban kasar.

KU KARANTA: Yariman Zazzau, Munir Ja'afaru ya taya Ahmed Bamalli murnar zama sabon Sarkin Zazzau

Ana sa ran Akeredolu zai fafata da ƴan takara daga sauran jam'iyyu amma wanda ya fi ɗaukan hankali shine Eyitayo Jegede na jam'iyyar PDP.

Mataimakin gwamnan mai ci yanzu, Agboola Ajayi, shima wani muhimmin ɗan takarar ne a ƙarƙashin jam'iyar Zenith Labour Party (ZLP).

A wani labarin daban, Gwamnatin tarayya ta bada umurnin masu amfana da shirin N-Power na Batch A da B da ba su samu kudadensu na watanni baya ba su tafi ofisoshin wakilansu na jihohi domin sake tantance su.

Ministan jin kai da kare afkuwar balai, Sadiya Umar Faruk ce ta bada wannan umurnin a ranar Talata kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel