Yariman Zazzau, Munir Ja'afaru ya taya Ahmed Bamalli murnar zama sabon Sarkin Zazzau

Yariman Zazzau, Munir Ja'afaru ya taya Ahmed Bamalli murnar zama sabon Sarkin Zazzau

- Mohammed Munir Ja'afaru, Yariman Zazzau ya taya sabon sarki Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli murna

- Yariman na Zazzau da ke cikin masu neman sarautar yace ya amince da nadin Bamalli a matsayin ikon Allah

- Ya mika godiya ga magoya bayansa tare da addu'ar Allah SWT ya yi wa sabon sarki jagora

Yariman Zazzau Mohammed Munir Ja'afaru ya taya Ahmed Nuhu Bamalli murna bisa naɗin da aka masa matsayin sabon sarkin Zazzau.

Munir Ja'afaru ya taya Ahmed Bamalli murnar zama sabon Sarkin Zazzau
Munir Ja'afaru ya taya Ahmed Bamalli murnar zama sabon Sarkin Zazzau. Hoto: @daily_nigerian
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yadda rundunar sojojin Najeriya za ta yi nasarar yaƙi da Boko Haram - Zulum

A ranar Laraba 7 ga watan Oktoban 2020 ne Gwamna Nasiru El-Rufai ya amince da nadin Ahmed Bamalli a matsayin sabon sarki don maye gurbin Dr. Shehu Idris da ya rasu a ranar 20 ga watan Satumba.

Da ya ke martani kan naɗin cikin sanarwar da ya fitar a ranar Laraba, Yariman Zazzau wadda ke cikin masu neman sarautar Zazzau ya amince da naɗin Bamalli a matsayin ƙaɗdara ta Allah.

Ya kuma yi addu'ar, "Allah SWT ya yi wa sabon sarki, ya kawo cigaba da zaman lafiya ga al'ummar masarautar."

KU KARANTA: Buhari ba shi da ikon sauya fasalin tsarin mulkin Najeriya - Tanko Yakasai

Ya ce, "Cike da godiya ga Allah SWT, na samu labarin naɗin Magajin Garin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau ga Gwamna Nasir El-Rufai ya yi.

"Ya zama dole dukkanmu mu yarda da ikon Allah mu taya sabon sarki Mai Girma Ambasada Nuhu Bamalli murnar nadin da aka masa.

"Allah ya yi masa jagoranci ya samar da zaman lafiya da cigaba ga al'ummar mu. Allahumma Amin.

"A madadin kai na, iyali, abokai da magoya na, ina son mika godiya ta gare ku bisa goyon baya da addu'a.

"Muna matukar godiya."

A wani labarin daban, Gwamnatin tarayya ta bada umurnin masu amfana da shirin N-Power na Batch A da B da ba su samu kudadensu na watanni baya ba su tafi ofisoshin wakilansu na jihohi domin sake tantance su.

Ministan jin kai da kare afkuwar balai, Sadiya Umar Faruk ce ta bada wannan umurnin a ranar Talata kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164